Wani jigo a jam’iyyar PDP a jihar Kaduna Dakta Mustapha Aliyu, ya gardadi Sanata Uba Sani, dan takarar gwamnan APC da ya bi a hankali kan zabar Hadiza Balarabe a matsayinta na musulma kuma wace za ta yi masa mataimakiya.
In ba a manta ba, a ranar 3 ga watan Yuli ne Uba Sani ya dauko Hadiza wacce a yanzu ita ce mataimakiyar gwamnan jihar Nasir El-Rufai don tunkarar zaben 2023.
- Osun 2022: An ga Wasu Na Yawo Da Bindigu A Osogbo
- INEC Ta Mayar Da Martani Kan Zargin Birne Katukan Zabe A Gidan Wani Babban Dan Siyasa A Ribas
Aliyu ya sanar da cewa, ya kamata a yi wa kowa adalaci a jihar wajen dauko mataimaki wanda ya kamata ya kasance Kirista.
“Kowane irin kwarewa Hadiza ke da shi, amma idan aka zo maganar shugabanci, kamata ya yi a yi wa ko wanne bangare adalaci.
“An san jihar kaduna a matsayin jiha mai addinai biyu, wato addnin musulunci da kuma na kirsitanci, inda ya kara da cewa, Nasir El-Rufai ne ya kirkiro da tsarin na daukar musulmi a matsayin mataimaki a jihar.