‘Yan bindiga da kuma ‘yan kungiyar ta’adda ta Ansaru sun fafata a tsakaninsu a karamar hukumar Birnin-Gwari da ke a jihar Kaduna.
An ruwaito cewa, ‘yan bindigar sun kai wa ‘yan kungiyar harin ne a lokacin da suke kan yi wa mutane wa’azi, inda suka bude wuta hakan ya janyo mutuwar wasu mutane biyu.
- Hajjin Bana: Wani Malamin Nijeriya Ya Rasu A Saudiyya
- Jam’iyyar APC Ta Rusa Kungiyoyin Yakin Zaben ‘Yan Takara
‘Yan bindigar sun dira a kauyen Damari ne da ke mazabar Kazage, wanda idan ba a manta ba ‘yan Ansarun sun jima da mayar da kauyen a matsayin wajen zamansu.
Shugaban kungiyar masarautar (BEPU) Ishaq Usman Kafai, ne ya tabbatar da hakan, inda ya sanar da cewa, sun shafe awa suna yin artabun a tsakaninsu.
Ya ce, a lokacin da abin ya auku ‘yan Ansaru na dauke da makamai, amma ‘yan bindigar suka ci karfinsu, inda ya kara da cewa, a lokacin artabun, an kona wani shago da ababen hawa biyu tare da kone wani asibiti mai zaman kansa.
Sai dai ya ce, bai san adadin ‘yan bindigar da na ‘yan Ansaru da suka samu raunuka ba.
An ruwaito cewa, daruruwan kauyawa da ke zaune a kauyen ciki har da mata da yara suka arce a lokacin karan-battar na kungiyoyin biyu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Mohammed Jalige, bai fitar da wata sanarawa kan artabun kungiyin biyu ba.