Farfesa Kabir Ahmed da ake yi wa laKabi da Abu Bilal ya bambanta da sauran Farfesoshi a Nijeriya, wadanda ke dogara kawai da sana’ar koyarwa a jami’o’i, shi a nasa bangare yana gudanar da sana’ar walda a matsayin sana’a ta biyu a garin Zariya da ke arewacin kasar.
Ana kallon sana’ar walda a matsayin karamar sana’a musamman a Nijeriya, lamarin da ya sa labarinsa ya bai wa mutane da dama mamaki, musamman abokan sana’arsa, bayan ya bude warin gudanar da sana’ar.
- Ɗaliban Jami’ar Jihar Nasarawa 2 Sun Mutu A Yayin Turmutsutsun Karɓar Abincin Tallafi
- Wuraren Kiwo: Fulani Sun Yi Murna Da Matakin Shugaban Kasa – Ngelzarma
“Bana jin wata shakkar kasancewata mai walda duk da cewa ni Farfesa ne, saboda ina samun kudi ta hanyar sana’ar,” kamar yadda ya bayyana wa BBC.
Malamin jami’ar mai shekara 50 – wanda ke duba daliban da ke bincike a tsangayar koyar da injiniyanci a jami’ar Ahmadu Bello da Zariya, ya kwashe shekara 18 yana koyarwa tare da wallafe-wallafen littafai.
Abu Bilal ya ce yana da kyau mutane, musamman wadanda suka kammala karatu, su rika fadada tunaninsu kan yadda za su samu abin dogaro da kawunansu.
“Ilimi ba zai hana ka gudanar da irin wadannan sana’o’i ba, na yi mamakin yadda mutane musamman wadanda ke da digiri na farko ke kallon irin wadannan sana’o’i a matsayin kankanci.”
Kalamansu sun yi daidai da wani rahoto da ya ce fiye da kashi 40 na wadanda ke kammala jami’a ba sa samun aikin gwamnati a Nijeriya, kasar da ta fi kowace yawan al’umma a nahiyar Afirka.
Malamin ya bude wani karamin wajen walda a Zariya kusan shekara 20 da suka gabata.
A shekarar 2022, shekara guda bayan ya zama farfesa, ya koma wani sabon wur mai girma, inda ya bude sana’o’i masu yawa a garin.
Hakan ya ba shi damar sayo karin kayan aiki masu yawa, tare da gudanar da manyan ayyuka, inda kwastomominsa ke zuwa don yi musu abubuwa kamar kofar karfe da tagogi da sauran abubuwa.
“Na kan yi sana’a komai kankantarta, ko da kofa guda ce nakan yi mata walda cikin jin dadi domin a biyani,’” in ji shi.
Tun yana matashi, Farfesan ya ce yake ta sha’arwar gyaran abubuwa irinsu radiyo, lamarin da ya kai shi ga karatun fanin injiniya, “Sai dai abin mamakin, sai na fahimci injiniyanci da ake koyarwa a jami’a a takarda ne kawai, don haka ina bukatar wurin da yi rika aiwatar da shi a aikace,” in ji shi
Wannan sha’arwa ce ta sa na bude shago don fara walda’”.
Ba wai don cika burinsa ne kawai ya bude shagon ba, sana’ar na taimaka masa wajen samun abin biyan bukatunsa na yau da kullum.
Farfesa Abu Bilal ya ce sana’arsa ta walda na ba shi damar samun abin biyan bukatunsa, lamarin da ya sa har ya samu damar sayen karamar motarsa mai kyau kirar ‘Mercedes’.
“A lokacin da malaman jami’a muka tsunduma yajin aiki na kusan wata takwas a shekarar 2022, kuma gwamnati ta daina biyanmu albashi, ban rasa abin kashewa ba saboda wannan sana’ar, kuma wasu daga cikin takwarorina kan zo wajen domin in taimaka musu’”.
Farfesa Abu Bilal na fatan jan ra’ayin sauran mutane irinsa da su rungumi sana’o’i irin nasa. Yana da yara 10 a shagon masu shekaru tsakanin 12 zuwa 20, da ke samun kwarewa kan sana’ar a wajen shehin malamin jami’ar.
Wadanda ba su je makaranta da rana ba, ke kula da shagon da rana idan malamin yana jami’ar.
Masu koyon sana’ar kan yi shekara guda a shagon Farfesan – sannan su je su bude nasu wuraren sana’ar bayan ya yayesu
“Na koyi abubuwa da dama a wurin, a yanzu ina iya yin abubuwa masu yawa ta hanyar walda,” in ji wani matashi mai shekara 18 da ke koyon sana’ar a wurin.
“Duk da cewa mu masu koyon sana’a ne, yana ba mu naira 10,000 a kowane wata, baya ga kudin abinci da yake ba mu a kowacce rana”.
Shehin malamin jami’ar ya kuma ce yana fatan ‘ya’yansa biyar su koyi sana’r tasa domin dagora da kawunansu, “Nakan zo da su wajen sana’ar a ranakun da babu makaranta domin su ga yadda ake gudanar da wannan sana’ar, ina so su koyi sana’ar saboda wata rana”.
A ganin Farfesa Abu Bilal wannna sana’ar tasa ba za ta hana shi sauke nau’in koyarwa da yake yi a jami’a ba, saboda shi ma aikin koyarwa aiki ne da yake da sha’awarsa sosai ”Ina son koyar da ilimi.”