Shugaba Bola Tinubu, ya ce daga yanzu duk wanda aka kama a matsayin mai satar mutane za a dauke shi a matsayin dan ta’adda.
Tinubu ya jaddada aniyar gwamnatinsa na yakar ‘yan bindiga, ta hanyar amfani da karfin soji.
- Tarihi Da Darussa 7 Daga Yaƙin Badar Da Aka Gwabza Ranar 17, Ga Ramadan
- Wadanne Sakonni Ne Ziyarar Shugaban Nauru Ta Farko A Kasar Sin Ta Isar Bayan Maido Da Huldar Jakadanci?
Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake buda baki da alkalan gwamnatin tarayya a ranar Talata a fadar shugaban kasa da ke Aso Rock.
”Dole ne mu dauki masu garkuwa da mutane a matsayin ‘yan ta’adda. Su matsorata ne. Wulkantattu ne. Suna kai hari kan marasa karfi.
“Suna zuwa makarantu suna sace yara suna haifar da rashin jituwa. Dole ne mu dauke su a matsayin ‘yan ta’adda don mu kawar da su, kuma na yi muku alkawarin za mu kawar da su.”
Wannan kalamai na Tinubu na zuwa ne bayan ceto daliban Kuriga da hukumomin tsaro suka yi a ranar Lahadi.
A gefe guda kuma gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare, ya gana da Tinubu a ranar Talata, don tattaunawa kan matsalar tsaro da ta addabi jiharsa.
Ko a baya gwamnan ya yi irin wannan zama da sauran hukumomin tsaro domin kai wa jihar dauki.