Mahaifiyar marigaya Ummita, Fatima Zubairu ta nuna godiya ga Allah kan hukuncin da aka yanke wa dan China da ya kashe mata ‘yarta.
Mahaifiyar ta bayyana haka ne biyo bayan hukuncin da wata babbar kotu a Jihar Kano, ta yanke hukuncin a ranar Talata.
- Tarihi Da Darussa 7 Daga Yaƙin Badar Da Aka Gwabza Ranar 17, Ga Ramadan
- Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Samar Da Daidaitaccen Tunanin Raya Kasa
“Na gode wa Allah da ya nuna min wannan rana ina matukar farin ciki,” in ji ta.
Mai sharia Sunusi Ado Ma’aji ne, ya yanke hukuncin bayan kama saurayin Ummita, Frank Geng da laifin aikata kisan kai.
Idan za a iya tunawa dai an kama tare da tsare Geng-Quangrong ne bayan kama shi a watan Satumban 2022 da laifin kashe Ummita mai shekaru 22.
Bayan yanke hukuncin, Kwamishinan Shari’a na jihar Kano, Haruna Dederi, ya bayyana wa manema labarai cewar an kammala bincike sannan an kama shi da laifin kisa.
“Shi ne alkalin wannan kotu ya yi wannan hukunci na kama Frank da laifin kisa kuma hukuncin kisa ne duk wanda ya yi kisa shi ma hukunci a kashe shi, kuma ya yi hukuncinsa a haka cewa za a rataye shi ne har sai ya daina motsi ya rasa rai abin da alkali ya fada kenan.
“Ita sharia tana da farko tana da karshe, abubuwan da aka iya bi aka gano kafin shari’ar da su ne aka kafa hukunci sannan abubuwan da suka gabata da shi ne aka gabatar da wannan hukunci kuma mutum ba zai aikata laifi ba a kuma bar shi yana yawo ba,” cewar Dederi.