Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya biya tallafin man fetur domin a sayar wa manoma kowace lita a kan Naira 500 maimakon 730 a Jihar Borno.
Manoman da za su ci gajiyar tallafin su ne na Damasak, da ke Arewacin jihar; don kara habbaka noman rani.
Kazalika, gwamnan ya kaddamar da tashar samar da ruwan sha mai karfin dawakai 90 duk dai a garin na Damasak, a lokacin ya kai ziyarar aiki garin.
- Gwamnan Bauchi Ya Biya Kashi 50 Na Karin Kudin Kujera Ga Alhazan 1652
- Zulum Ya Rabawa ‘Yan Sa Kai Da Mafarauta 5,523 Naira Miliyan 255 Da Buhunan Shinkafa 5,513
Wannan tasha ta samar da ruwan sha mai dauke da karfin dawakai 90, an tanadar mata hasken wuta na sola mai amfani da hasken rana mai karfin nauyin kilowatt 115, domin yin ban ruwa ga wasu bangarori guda uku tare da samar da adadin ruwan da ya doshi lita 225 a duk dakika daya da kuma fitar maki 105, wanda ya kunshi kadada 125 na wurin noman shinkafa.
Zulum ya sanar da cewa, gwamnatinsa za ta sauya akalarta ne daga ci gaba da rabon kayan abinci ga al’ummarta zuwa karfafa wa manoma guiwa tare da ba su dukkanin gudunmawar da ta dace, domin inganta harkokin noma a fadin jihar.
“Magance matsalolinmu na dan kankanin lokaci, ba zai taba dawwama ba, sannan ci gaba da yin rabon kayan abinci ga mutane, musamman ‘yan gudun hijira wadanda suke zaune a sansaninsu, shi ma ba zai taba dorewa ba. Don haka, babu abin day a fi dacewa da mu; illa mu canza tinaninmu daga magance matsalolinmu na dan kankanin lokaci zuwa na tsawon lokaci, wanda shi ne kadai masalaha a gare mu; wannan kuwa ba wani abu ba ne illa NOMA,” in ji Zulum.
Har ila yau, ya bayyana aniyarsa ta samar da man fetir kimanin lita miliyan daya ga manoma, wanda a cewar tasa za a rarraba shi zuwa kowace karamar hukuma da ke fadin jihar.