Jarumar Fina-finan Hausa ta Kannywood, Hadiza Muhammad wadda akafi sani da Hadizan Saima ta bayyana dalilin da yasa bata wasa da cin abinci a duk lokacin da take tsaka da daukar shirin fim.
Hadiza yayin da take amsa tambayoyi a wata hira da tayi da Ibrahim Mandawari a cikin shirinsa na Mushakata, ta bayyana cewa, “a duk lokacin da take tsaka da daukar fim takan yi kokarin samun abinda ta saka a bakin salati saboda abinci shine rayuwa.”
- Ba Shakka Kamfanonin Ketare Za Su Ci Riba In Suka Zuba Jari Da Aiwatar Da Ayyukansu A Sin
- An Kama Wani Matashi Mai Shekaru 25 Bisa Zargin Kashe Abokinsa A Kano
Mai gabatar da shirin na Mushakata, Ibrahim Mandawari ya tambayi Hadiza wani abu da yace masoyanta zasu so sani akan maganar da ake yadawa na cewa, idan zata hakura da komai ba zata hakura da abinci yayin daukar fim ba.?
Sai ta amsa da cewa, Eh! hakane gaskiya bana wasa da cin abinci yayin daukar kowane irin shiri saboda ko babu komai akwai yiwuwar kamuwa da cutar gyambon ciki ga duk wani mutum da yake wasa da cin abinci.