Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, ya bayyana cewa samar da tallafi bai kasance hanyar magance matsalolin tattalin arziki da ke samun Nijeriya ba.
Gwamna Diri wanda ya shaida hakan a lokacin da ke jawabi a wajen bikin Easter a cocin St. Peter’s Anglican Church, Sampou da ke karamar hukumar Kolokuma/Opokuma a Jihar Bayelsa.
- Sin Ta Yi Kira Ga Kasa Da Kasa Da Su Taimakawa Gwamnatocin Kasashe Masu Fama Da Rikici Wajen Tabbatar Da Rayuwar Yara A Dukkan Fannoni
- Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya
Gwamnan ya ce duk da shi ba wai yana sukar tallafin ba ne, sai dai shi ya fi gamsuwar ya saita abubuwa da tsare-tsaren da suka dace da za su kai ga shawo kan matsalar tattalin arziki da ake fuskanta.
Ya ce gwamnatinsa tana samar da shirye-shirye da manufofin da za su kawo matakin samar da abubuwan yi ga jama’a masu nisan zango ba kawai tallafi da zai kare a dan kankanin lokaci ba.
A cewarsa, gwamnatinsa ta dukufa wajen magance karancin ma’aikata da matsalar koyon sana’ar hannu ta hanyar kirkirar kwalejojin fasaha a kananan hukumomi takwas, bijiro da shirye-shiryen koyar da sana’ar hannu, gina manya da kananan titina domin hade birane da sauran tsare-tsaren da suke taimaka wa tattalin arzikin al’umma.
Ya ce, “Babu ta yadda za a yi a duk duniya a ce gwamnati ta maka komai da komai. Mu shiga a dama da mu a harkokin kasuwanci.
“Ku yi kokarin cin gajiyar shirye-shiryenmu guda hudu na koyar da sana’o’i hakan zai taimaka wa kawukanmu da kuma Jihar Bayelsa. Ta wannan hanyar ce matasa za su kasance masu amfanuwa.”
Ya bukaci al’umma da su koyi da kwawawan dabi’un Annabi Isa wajen kyautata rayuwarsu na yau da gobe.