Ademola Nurudeen Jackson Adeleke dan siyasar Nijeriya ne kuma dan kasuwa, Sanata ne mai wakiltar mazabar Osun ta yamma daga 2017 zuwa 2019.
Ya fito ne daga dangin Adeleke na Ede a jihar Osun.
- An Yi Wa Kasurgumin Dan Bindiga Sarauta A ZamfaraÂ
- ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mai Juna Biyu A Kaduna
Ya tsaya takarar gwamnan jihar Osun a shekarar 2022 ya kuma doke gwamna mai ci, Adegboyega Isiaka Oyetola wanda ya kayar da shi a zaben gwamnan jihar Osun na 2018.
1. An haifi Ademola Adeleke a ranar 13 ga watan Mayu 1960, yana da shakaru 62.
2. Adeleke dan kasuwa ne; ya yi aiki a matsayin babban darakta na kamfanin Guinness Nigeria Plc daga 1992-1999.
3. Adeleke ya fara harkar siyasa ne a shekarar 2001 tare da dan uwansa marigayi Sanata Isiaka Adeleke wanda ya rasu a watan Afrilun 2017.
4. An gurfanar da Adeleke a gaban babbar kotun Osogbo kan zargin laifin yin jabun shaidar makarantar sakandare da kuma sakamakon jarrabawar WAEC, inda aka bukaci a soke takararsa ta gwamna.
5. Adeleke na da yara biyar da suka hada da B-Red, sannan kawu ne ga fitaccen mawakin nan, Davido.