A shekarun baya bayan nan, kasar Amurka tana ta neman yin karin tasiri a nahiyar Afirka. Bisa wannan yunkuri, ana ta samun dimbin rahotanni daga kafofin yada labarai na kasashen yamma dake nuna wai “Amurka da Sin na takara da juna a nahiyar Afirka”, da “ kasashen yamma na takara da kasashen Sin da Rasha, da wasu kasashen dake gabas ta tsakiya, don kwatar damar kulla huldar kawance tare da kasashen Afirka”, da dai sauransu daga kafofin yada labarai na kasashen yamma. Hakan na sa mutum tsammanin cewa, watakila kasashen Afirka ba za su iya kaucewa daukar wani bangare, a tsakanin karfin dake takara da juna a duniya ba. Sai dai abun tambaya a nan shi ne ko kasashen na Afirka suna son yin haka?
Wata kila a ki yin zabi, ko ma a magance yarda da ra’ayin maida kasashen yamma cibiyar duniya, da neman dakile saura, zai fi dacewa ga kasashen Afirka, don neman biyan bukatunsu na kare moriyar kai.
- Xi Ya Aike Da Sakon Ta’aziyya Ga Shugaban Kasar Mozambique
- Xi Jinping Ya Yi Shawarwari Tare Da Takwaransa Na Indonesia
A wajen taron musayar ra’ayi tsakanin Sin da Afirka ta fannin wayewar kai karo na 3, da ya gudana a kwanan nan a birnin Beijing na Sin, masana da jami’ai na kasashen Afirka da na kasar Sin sun sake jaddada muhimmancin ra’ayin diplomasiyya na magance daukar wani bangare. Kana wannan ra’ayi ya zama daya da tunanin hadin gwiwar Sin da Afirka, wato maimakon nuna son kai da neman dakile saura, a bude kofa domin kowa ya iya halarta, da aiwatar da tunani na kasancewar dimbin bangarori masu fada a ji a duniya.
Taron na wannan karo ya kunshi dandalin tattaunawa guda 2, daya ya shafi musayar ra’ayi cikin daidaito, kan al’adu da tunani na Sin da Afirka. Daya kuwa ya shafi musayar ra’ayin raya kasa, don aza harsashin hadin gwiwar nan gaba. Kana babbar ma’anar taron ita ce, kamar yadda Rahamtalla M. Osman, jakadan kungiyar tarayyar kasashen Afirka AU a kasar Sin ya fada, “Daidaita ra’ayi da magance bahaguwar fahimta, ta yadda za a karfafa fahimtar juna da girmama juna da hadin gwiwa, ta hanyar yin musayar ra’ayi”.
Nufinsa shi ne, ta hanyar tattaunawa, ake neman kawar da shingen tunani da ra’ayoyi marasa dacewa, da kasar Amurka da wasu kasashen dake yammacin duniya suka sanya wa kasashen Afirka da kasar Sin, da sauran kasashe masu tasowa. Ta yadda za a samu tunani na kai, da yiwuwar dogaro da kai, da samun ci gaban kasa mai dorewa.
Irin wannan cudanyar ra’ayi mai daraja, ta sa ana ta samun tunani masu muhimmanci a tarukan musayar ra’ayi, tsakanin Sin da Afirka ta fannin wayewar kai, da aka taba gudanarwa a baya.
Misali, Rahamtalla M. Osman, jakadan kungiyar kasashen Afirka AU a kasar Sin, ya taba bayyanawa a madadin kungiyar AU cewa, ya kamata a daina ta da rikici tsakanin mabambantan wayewar kai, da neman tabbatar da kasancewarsu tare, da daina ganin al’adun wasu sun fi na wasu, tare da karfafa cudanya, da koyi da juna tsakanin wayin kai daban daban.
Sa’an nan a nasa bangare, shugaban cibiyar nazarin manufofin kasashen Afirka na kasar Kenya Peter Kagwanja, ya taba bayyana cewa, “Aikin zamanantar da kasar Sin, da yadda ake neman zamanantar da kasashen Afirka sun bambanta, amma za a iya kaiwa ga cimma buri guda daya. Saboda haka, ci gaban kasar Sin ya karfafa gwiwar jama’ar kasashen Afirka. Mu ma muna son tabbatar da zamanantarwa bisa dogaro da karfin kanmu.”
Ban da haka, Charles Onunaiju, darektan cibiyar nazarin kasar Sin ta kasar Najeriya, ya taba bayyana cewa, babbar matsala da kasashen Afirka suke fama da ita, ita ce talauci. Kana babban dalilin da ya sa muke kokarin zamanantar da kanmu shi ne don biyan bukatun jama’a. A cewarsa, “ Ya kamata mu koyi dabarun da kasar Sin ta samu, a kokarinta na raya kai. Sa’an nan mu yi kokarin ganowa da daidaita muhimmin bangare dake bukatar a daidaita shi, yayin da muke neman raya tattalin arziki da zaman al’umma na kasashen Afirka. ”
Ta jawabansu za mu iya ganin cewa, jami’ai da masana na kasashen Afirka, sun fara dora karin muhimmanci kan kasancewar mabambantan wayewar kai tare (maimakon samun takara da rikici a tsakaninsu), da dogaro da kai a kokarin neman ci gaban kasa ( maimakon rungumar wai “daidaitaccen tsari” na kasashen yamma na tabbatar da ci gaba), da kokarin biyan bukatun jama’a (maimakon dora nauyi kan tsarin kasuwa mai ‘yanci), da sauran tunani, wadanda suka sha bamban da ra’ayoyin kasar Amurka, da na sauran kasashen yammacin duniya.
Hakan ba wani abun ban mamaki ba ne, saboda fasahohin da kasar Sin ta samu a kokarin raya kanta, sun nuna mana cewa, dole ne a samu tunani na kai, kafin a kai ga samun cikakken ‘yancin kai. Kana ya kamata a bi hanyar raya kasa ta musamman, da ta dace da yanayin da kasa ke ciki, har a kai ga samar da hakikanin ci gabanta. (Bello Wang)