Kokarin da gwamnatin Nijeriya take na fatattakar cutar tarin fuka (TB) ya ci gaba da samun fuskantar matsaloli. Wani rahoton da aka fitar kwanan nan daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya nuna cewa, kasar nan ce a kan gaba na yawan masu cutar ba yankin Afirka, ita ce kuma ta 6 a jerin kasashe masu fama da cutar a duniya gaba daya.Wannan karin takaicin kuma shi ne cutar ke kashe ko wane mutum daya a duk minti biyar duk kuwa da cewa ana iya rigakafinta, Kididdiga ta nuna cewa cutar na kashe mutum 97,900 duk shekara a Nijeriya.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta nuna matukar damuwarta a kan yadda ake samun karuwar masu fama da cutar a kasar. Ta ci gaba da nuna damuwar ne saboda Nijeriya ke da kashi 23 na mace-mace da ake yi a Afrika sanadiyyar cutar Fukar, duk da tana da cibiyar kula da masu cutar 50 a fadin kasar, ana iya samar da hanyoyin kariya na jinyar masu fama da cutar ba tare da wata wahala ba.
- PSG Ta Shiga Gaban Chelsea Wajen Neman Daukar Victor OsimhenÂ
- Sin: An Fitar Da Tsarin Tallafin Kudade Domin Bunkasa Ci Gaba Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba
Idan za a iya tunawa an fara shirin gangamin yaki da cutar fuka da kuturta a Nijeriya (NTBLCP) ne tun a shekarar 1989. Amma kuma wannan kokarin bai haifar da da mai ido ba, musamman ma idan aka yi la’akari da rahottanin da ke shigo wa daga sassan kasa inda suke nuna babu wani ci gaba mai karfafa gwiwa, a daidai lokacin da ake bikin ranar cutar fuka ta duniya an samu rahottanin karuwar yaduwar cutar a tsakanin al’umma.
A duk fadin kasar, labarin daya ne babu jiha ko ko wata karamar hukumar da ta tsira daga cutar inda take kisa ba kakkautawa.Bayani ya nuna cewa, mutum 7,000 ne suka mutu sanadiyyar kamuwa da cutar a Jihar Kros Ribas kadai. Cutar ta fi kamari ne a kananan hukumomin Kalaba ta Yamma, Ogoja, Boki da kuma Yakurr.
Haka nan ma mutum 7,496 suka kamu da cutar a jihohin Inugu da Borno, yayin da kwamishinan lafiya na Jihar Kwara, Dokta Amina El-Imam, ta bayyana cewa, cutar tarin Fuka ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 1,869 a shekarar 2023. Haka kuma kwamishinan Lafiya na Jihar Inugu Farfesa Ikechukwu Obi, ya tabbatar da cewa mutum 2,496 suka kamu da cutar tarin Fuka a jihar a shekarar 2022.
A shekarar 2023, gwamnatin jihar Borno ta bakin kwamishinan lafiya na jihar Farfesa Baba Malam-Gana, ta ce an samu masu cutar tarin Fuka 5,000 ana kuma zargin cewa fiye da mutum 10.000 suke dauke da cutar a fadin jihar. Bayanin ya kuma nuna cewa, a Jihar Kano an samu masu fama da cutar har mutum 26,271 a shekarar 2022.A zangon karshe na shekarar 2022, an samu barkewar cutar har sau 9,941 wannan shi ne mafi yawa a tarihin cutar a Nijeriya.
A ra’ayin wannan jaridar, abin takaici ne yadda yawan wadanda cutar ya kashe ma fi yawan wadanda cutar korona ta kashe gaba daya, wannan kuma yana faruwa ne duk da majalisar dinkin duniya ta ayyana shekarar 2030 a matsayin shekarar da za a kawo karshen cutar gaba daya a fadin duniya.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa, wani kwayar cutar mai suna ‘mycobacterium tuberculosis bacteria’ ke haifar da cutar tarin fuka, cutar na kai hari huhu ne tana kuma iya shafar wasu sassan jiki gaba daya.
Wani abin mamaki anan shi ne yadda kashi goma na masu fama da cutar basu nuna cikakken alamu amma kuma daga nan sai kaga cutar tana yin ajalin mutum in har ba a dauki matakin da ya kamata ba.
Muna sane da cewa, ko kashi 17 na kudaden da aka ware wa yaki da cutar Fuka baya samun fitowa daga asusun gwamnati. Duk da haka ya kamata cututtuka da ke zama barazana ga rayuwar al’umma kamar cututtukan fuka, maleriya, kanjamau da sauransu a dauki matakin dakile yaduwar su gaba daya.
A mastayinmu na gidan jarida muna da ra’ayin cewa, wannan shi ne lokacin da ya kamata a kara kaimi wajen yaki da cutar tarin fuka ta hanyar kara hanyoyin fadakar da al’umma illar da hanyoyin kare kai daga kamuwa da ita.
Damuwarmu kuma ita ce al’umma da dama basu san komai ba dangane da cutar da hanyoyin kare kai daga gareta. Wannan yana nuna cewa, dole a karfafa fadakar da al’umma hanyoyin kariya tare da gagauta gano cutar da gaggawa.
Ya kamata gwamnatocin jihohi da sauran masu ruwa da tsaki su hada hannu don yin gangamin yaki da cutar ta hanyar kara zuba kudaden aiki da karfafa malaman lafiya da ke jinyar masu dauke da cutar. Kungiyoyi masu zaman kansu na da tasu gudunmawar da za su bayar domin samun ita nasarar.