ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, July 16, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yaki Da Sake Yaduwar Cutar Tarin Fuka

by Leadership Hausa
2 years ago
Tarin

Kokarin da gwamnatin Nijeriya take na fatattakar cutar tarin fuka (TB) ya ci gaba da samun fuskantar matsaloli. Wani rahoton da aka fitar kwanan nan daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya nuna cewa, kasar nan ce a kan gaba na yawan masu cutar ba yankin Afirka, ita ce kuma ta 6 a jerin kasashe masu fama da cutar a duniya gaba daya.Wannan karin  takaicin kuma shi ne cutar ke kashe ko wane mutum daya a duk minti biyar duk kuwa da cewa ana iya rigakafinta, Kididdiga ta nuna cewa cutar na kashe mutum 97,900 duk shekara a Nijeriya.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta nuna matukar damuwarta a kan yadda ake samun karuwar masu fama da cutar a kasar. Ta ci gaba da  nuna damuwar ne saboda Nijeriya ke  da kashi 23 na mace-mace da ake yi a Afrika sanadiyyar cutar Fukar, duk  da tana da cibiyar  kula da masu cutar 50 a fadin kasar,  ana iya samar da hanyoyin kariya na jinyar masu fama da cutar ba tare da wata wahala ba.

  • PSG Ta Shiga Gaban Chelsea Wajen Neman Daukar Victor Osimhen 
  • Sin: An Fitar Da Tsarin Tallafin Kudade Domin Bunkasa Ci Gaba Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba

Idan za a iya tunawa an fara shirin gangamin yaki da cutar fuka da kuturta a Nijeriya (NTBLCP) ne tun a shekarar 1989. Amma kuma wannan kokarin bai haifar da da mai ido ba, musamman ma idan aka yi la’akari da rahottanin da ke shigo wa daga sassan kasa inda suke nuna babu wani ci gaba mai karfafa gwiwa, a daidai lokacin da ake bikin ranar cutar fuka ta duniya an samu rahottanin karuwar yaduwar cutar a tsakanin al’umma.

ADVERTISEMENT

A duk fadin kasar, labarin daya ne babu jiha ko  ko wata karamar hukumar da ta tsira daga cutar inda take kisa ba kakkautawa.Bayani ya nuna cewa, mutum 7,000 ne suka mutu sanadiyyar kamuwa da cutar a Jihar Kros Ribas kadai. Cutar ta fi kamari ne a kananan hukumomin Kalaba ta Yamma, Ogoja, Boki da kuma Yakurr.

Haka nan ma mutum 7,496 suka kamu da cutar a jihohin Inugu da Borno, yayin da kwamishinan lafiya na Jihar Kwara, Dokta Amina El-Imam, ta bayyana cewa, cutar tarin Fuka ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 1,869 a shekarar 2023. Haka kuma kwamishinan Lafiya na Jihar Inugu Farfesa Ikechukwu Obi, ya tabbatar da cewa mutum 2,496 suka kamu da cutar tarin Fuka a jihar a shekarar 2022.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Ƙasar Turkiyya Sun Nuna Jarumta Da Kare Dimokuraɗiyya Mafi Girma A Tarihi – Erdoğan

Lalata Da Ƙaramar Yarinya: Kotu Ta Yanke Wa Tsoho Mai Shekara 75 Hukuncin Ɗaurin Shekara 10 A Ribas

A shekarar 2023, gwamnatin jihar Borno  ta bakin kwamishinan lafiya na jihar Farfesa Baba Malam-Gana, ta ce an samu masu cutar tarin Fuka 5,000 ana kuma zargin cewa fiye da mutum 10.000 suke dauke da cutar a fadin jihar. Bayanin ya kuma nuna cewa, a Jihar Kano an samu masu fama da cutar har mutum 26,271 a shekarar 2022.A zangon karshe na shekarar 2022, an samu barkewar cutar har sau 9,941 wannan shi ne mafi yawa a tarihin cutar a Nijeriya.

A ra’ayin wannan jaridar, abin takaici ne yadda yawan wadanda cutar ya kashe ma fi yawan wadanda cutar korona ta kashe gaba daya, wannan kuma yana faruwa ne duk da majalisar dinkin duniya ta ayyana shekarar 2030 a matsayin shekarar da za a kawo karshen cutar gaba daya a fadin duniya.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa, wani kwayar cutar mai suna ‘mycobacterium tuberculosis bacteria’ ke haifar da cutar tarin fuka, cutar na kai hari huhu ne tana kuma iya shafar wasu sassan jiki gaba daya.

Wani abin mamaki anan shi ne yadda kashi goma na masu fama da cutar basu nuna cikakken alamu amma kuma daga nan sai kaga cutar tana yin ajalin mutum in har ba a dauki matakin da ya kamata ba.

Muna sane da cewa, ko kashi 17 na kudaden da aka ware wa yaki da cutar Fuka baya samun fitowa daga asusun gwamnati. Duk da haka ya kamata cututtuka da ke zama barazana ga rayuwar al’umma kamar cututtukan fuka, maleriya,  kanjamau da sauransu a dauki matakin dakile yaduwar su gaba daya.

A mastayinmu na gidan jarida muna da ra’ayin cewa, wannan shi ne lokacin da ya kamata a kara kaimi wajen yaki da cutar tarin fuka ta hanyar kara hanyoyin fadakar da al’umma illar da hanyoyin kare kai daga kamuwa da ita.

Damuwarmu kuma ita ce al’umma da dama basu san komai ba dangane da cutar da hanyoyin kare kai daga gareta. Wannan yana nuna cewa, dole a karfafa fadakar da al’umma hanyoyin kariya tare da gagauta gano cutar da gaggawa.

Ya kamata gwamnatocin jihohi da sauran masu ruwa da tsaki su hada hannu don yin gangamin yaki da cutar ta hanyar kara zuba kudaden aiki da karfafa malaman lafiya da ke  jinyar masu dauke da cutar. Kungiyoyi masu zaman kansu na da tasu gudunmawar da za su bayar domin samun ita nasarar.

Tarin
Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Tallafa Wa Yara Masu Buƙatu Na Musamman Shi Ne Burina
  • Leadership Hausa
    Dole Mata Su Rungumi Sana’o’i Domin Tsira Daga Takaicin Zamani —Ramatu Bello
  • Leadership Hausa
    Batun Dakile Shan Taba Sigari A Tsakanin Yara A Nijeriya
  • Leadership Hausa
    Har Yanzu Akwai Sauran Rina A Kaba Game Da Makomar Yara A Nijeriya

MASU ALAKA

‘Yan Ƙasar Turkiyya Sun Nuna Jarumta Da Kare Dimokuraɗiyya Mafi Girma A Tarihi – Erdoğan
Manyan Labarai

‘Yan Ƙasar Turkiyya Sun Nuna Jarumta Da Kare Dimokuraɗiyya Mafi Girma A Tarihi – Erdoğan

July 15, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga
Manyan Labarai

Lalata Da Ƙaramar Yarinya: Kotu Ta Yanke Wa Tsoho Mai Shekara 75 Hukuncin Ɗaurin Shekara 10 A Ribas

July 15, 2026
‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta, Jami’in NECO Da Ɗalibai A Kogi
Manyan Labarai

‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta, Jami’in NECO Da Ɗalibai A Kogi

July 15, 2026
Next Post
Sharhi: Lokaci Ya Yi Da Tinubu Zai Fuskanci Matsalolin Nijeriya

Barka Da Sallah: Shugabanni Sun Yi Kiran Amfani Da Darussan Ramadan

LABARAI MASU NASABA

Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo

Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo

July 15, 2026
Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta

Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta

July 15, 2026
Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya

Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya

July 15, 2026
Neman Raba-Gari Da Sauran Kasashe Zai Kawo Mummuann Tasiri Ga Bangarorin Da Abin Ya Shafa

Neman Raba-Gari Da Sauran Kasashe Zai Kawo Mummuann Tasiri Ga Bangarorin Da Abin Ya Shafa

July 15, 2026
Kevin Kelly: AI Na Iya Taimakawa Wajen Cimma Burin “Koyar Da Dalibai Da Kwazonsu”

Kevin Kelly: AI Na Iya Taimakawa Wajen Cimma Burin “Koyar Da Dalibai Da Kwazonsu”

July 15, 2026
Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

July 15, 2026
Sabbin Ministoci

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Tura Ƙarin Sojoji da ’Yansanda Zuwa Benuwe

July 15, 2026
GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

Atiku Ya Nuna Damuwa Kan Kasafin Naira Biliyan 6.44 Don Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026

July 15, 2026
Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

July 15, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.