A yayin da al’ummar Musulmi a fadin duniya suka kammala Azumin watan Ramadan na banar, sun gudanar da shagulgulan bikin karamar Sallah, sai dai wasu sallah ta zo musu ba kamar yadda suka saba fantamawa a baya ba.
LEADERHIP Hausa ta jiyo ra’ayoyin wasu mazauna Jihar Kaduna, musamman talakawa da kuma teloli kan irin yanayin yadda karamar Sallar bana ta zo masu duba da matsin rayuwa.
- Liu Yuxi Ya Halarci Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kan Sin Da Afirka Karo Na Uku
- Bikin Sallah: Ministan Yaɗa Labarai Ya Nemi ‘Yan Nijeriya Su Dawo Da Kyawawan Dabi’un Da Suka Jingine
Wata mai suna Aisha Usman, wadda mijinta ya rasu ya bar mata marayu hudu ta ce, Sallar bana ba ta zo mata yadda ta yi tsammani ba, saboda matsin tattalin arziki da talauci. Ta ce da ba ta samu tallafin abincin daga wurin jama’a ba, da ba ta san yadda za ta ciyar da marayunta.
Ta ce maganar dinka masu kayan Sallah ma ba ta taso ba, ina kokarin samu abincin da za su ci gaba da ci bayan kammala Azumin.
Ibrahim Sani ya ce, duk da cewa ana cikin yanayin matsin rayauwa, wata uku kafin fara Azumin ya fara tanadin abincin da iyalisa za su yi amfani da shi da Azumin. A cewarsa, duk da matsin na tattalin arziki, hakan nan ya kukata ya samu ya yi wa iyalisa kayan Sallah, saboda al’adace da aka saba.
Shi kuwa Saeed Muhammad ya ce, karamar Sallar bana ta zo masa a cikin wani irin yanayin da bai taba samun kaisa a ciki ba, domin kuwa, ya saba a duk shekara yana tallafa wa iyayesa da abinci, musamman a watan Azumi baya ga iyalansa da suka zamo masa wajibi, sannn kuma ya yi masu dinke-dinken suturar Sallah.
Ya ce sai dai a bana, saboda irin halin kuncin rayuwa da al’ummar kasar nan suka tsinci kansu a ciki, abun sai dai kawai ya ce sun gode wa Allah tun da ya bar su da rai da lafiya har kuma sun samu damar azumtar watan Ramadan.
Mustapha Musa ya ce, “Ni a yanzu ba na batun dinkin Sallah na yara, domin abun da ke gabana shi ne, in tanadar masu da abincin da za su ci a Sallar da kuma bayanta.”
A bangaren wasu teloli kuwa, akasarinsu sun ce bana ba harka domin Sallar ta zo masu a cikin bazata.
Daya daga cikinsu, Adamu Ibrahim ya ce, “A bana ban samu yawan aikin dinkuna da na saba samu a baya ba, amma ina ganin matsin tattalin arziki da ya addabi jama’a ne, musamman talakawa, shi ya sa ban samu yawan tulin aikin dinki da na saba samu a shekarun baya ba, amma Alhamdulillahi ba laifi na samu aikin dinkuna wadanda za su toshe min wasu kafa na ciyar da iyalina.”
Shi kuwa Sani Kabiru ya danganta rashin samun masu kawo masa aikin dinkuna kan yadda wasu Musulman suka gwammace su siya wa ‘ya’yansu dinkakkun kayayyaki da ake sayarwa a kasuwa, wadanda ake yi wa lakabi da ‘Ishirun ka maraya’.Ya ce, hakan na da nasaba da yanayin matsin tattalin arziki da ake fuskanta a kasar.
Abudllahi Umar ya ce, “A Sallar bana, shagona ba masaka tsinke, saboda yawan aikin dinkunan da aka kawo min kusan wata biyu kafin fara Azumi, sai da na rufe karbar dinki saboda aikin da ke gabana ya yi min yawa. Sai duk da haka a bana ban samu rabin aikin da na ke samu ba.
A ra’ayin Garba Awwal ya danganta rashin samun abokan hulda ne kan tashin gwaron farashin dala, wanda hakan ya janyo hauhawan farashin kayan masarufi, musaman kayayyakin abinci, hakan ya rage wa jama’a kawo aikin dinki.
Ya ce yana gode wa Allah tun da an dan samu aikin da ba za a rasa ba, kuma yana ganin kila bayan Sallar idan an biya ma’aikata albashi za su kara samun aikin dinkin.
Shi kuwa Mahadi Rabe ya ce, wasu telolin saboda irin kudin da suke tsawallawa na yin dikin ne ya sa ba su samun aikin dinki mai yawa a bana ba. A cewarsa, ba ya ganin laifin ‘yan’uwasa teloli ko da sun tsawalla farashi dinki domin kayan aiki sun tashi.
A nata ra’ayin, Aisha Abubakar ta danganta rashin aikin dinkin ne kan rashin samun wadatacciyar wutar lantarki, wanda don gudun kar telolin su ba su kunya saboda rashin wutar lantarkin.
Ta kara dfa cewa saboda rashin wadatacciyar lantarkin dole ne sai sun sayi man fetur, wanda dole su kuma su kara cajin kudin aiki.
Ita ma Hau’uwa Yusuf ta bayyana cewa tana cikin hamdala, domin kuwa ba ta rasa samun aikin dinkin mata da yawa duk da yanayin halin kuncin da wasu jama’a suke a ciki.
Ta ce har rufe karbar dinki ta yi saboda ba ta so a bana ta janyo wa kaita zagi daga wurin masu kawo dinkin da ta iya kammala nasu ba.