Allah Ya yi wa hakimin Ikara, Injiniya Aminu Umar, daga masarautar Zazzau rasuwa.
Da yake tabbatar da rasuwarss a cikin wata sanarwa, Abdullahi Aliyu Kwarbai, shugaban yada labaran masarautar Zazzau, ya ce marigayin ya halarci hawan daushe da aka gudanar a Zariya ranar Juma’a.
- Ra’ayoyin Kasashen Duniya Game Da Harin Da Iran Ta Kaddamar A Kan Isra’ilaÂ
- Za A Gyara Wuta A Inganta Lafiya Da Ilimi Da KuÉ—in Tallafin Lantarkin Da Aka Janye – Ministan LabaraiÂ
Kuma yana daya daga cikin hakiman gundumomi da suka kai wa Sarkin Zazzau, Mallam Ahmed Nuhu Bamalli, ziyarar sallah.
A cewar sanarwar, “Ya rasu ne bayan ya halarci bukukuwan sallah da aka yi a Zariya.”
Marigayi Umar, ya fito ne daga zuri’ar marigayi Sarkin Dalhat, daga daular Barebari da ke suka mulki masarautar Zazzau.
Ya rasu ya bar mata da ’ya’ya da yawa.
Ya taba rike mukamkin shugaban gudanarwa na hukumar ruwa ta Jihar Kaduna.
Tuni aka yi jana’izarsa a garin Amaru da ke birnin Zariya.