Gwamnatin jihar Kano ta hana sana’ar adaidaita sahu daga kan karfe 10 na dare zuwa 6 na safe kuma dokar zata fara aiki ranar Alhamis 21 ga wannan watan.
Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da hakan bayan fitowa daga taron majalisar tsaro na jihar.
A cewar Kwamishinan, an dauki matakin ne domin kawo karshen matsalar tsaron da ake fuskanta a jihar.
A karshe Muhammad Garba ya shawarci matuka adaidaita sahu dake fadin jihar da su bawa jami’an tsaro hadin kai domin samun abinda ake so sannan dokar za tayi aiki ba sani ba sabo.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp