Gwamnatin Jihar Katsina ta rarraba motocin yaki ga jami’an tsaro domin shawo kan matsalar tsaro a kananan hukumomin da aka fi fuskantar hare-haren ‘yan bindiga.
Gwamnan jihar, Dikko Ummaru Radda ne ya kaddamar da rabon motocin a ranar Litinin.
- Babu Inda Mayaudara Da Mahassada Suka Taru Kamar Masana’antar Kannywood – Adam Zango
- Kalau Nake Babu Abin Da Ke Damun Kwakwalwata – Adam Zango
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Nasiru Mu’azu ya shaida wa manema labarai cewa sun yi la’akari ne da halin da ake ciki, kuma ita wannan mota mai sulke na taimaka wa wajen yakin da suke da ‘yan bindiga.
Gwamnatin ta raba motocin guda 10 ne ga jami’an ‘yan sanda da sojoji da kuma ‘yan sa-kai.
Ya ce kananan hukumomin da aka ba motocin sun hada da Jibiya da Safana da Danmusa da Kankara da Batsari da Faskari da Dandume da kuma Sabuwa.
Kwamishinan ya ce daman kananan hukumomin na da irin wadannan motoci, kawai kari ne aka yi masu saboda a kara samun ci gaba wajen yaki da ‘yan bindiga.