Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwaransa na kasar Iran Hossein Amir-Abdollahian sun tattauna ta wayar tarho a ranar 16 ga watan Afrilu dangane da takun saka tsakanin Isra’ila da Iran.
Amir-Abdollahian ya bayyana wa Wang cewa, matsayin Iran kan harin da aka kai a sashin karamin ofishin jakadancin Iran a birnin Damascus na kasar Syria. Yana mai cewa kwamitin sulhu na MDD bai bayar da martanin da ya dace kan wannan harin ba, kuma Iran na da hakkin kare kanta, a matsayin mayar da martani ga take hakkinta.
- Xi Ya Gabatar Da Ka’idoji Hudu Don Warware Rikicin Ukraine
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 12, Sun Ƙwato Babura Da Makamai A Zamfara
Amir-Abdollahian ya ce, halin da yankin ke ciki a halin yanzu yana da matukar muhimmanci, kuma Iran a shirye take ta kai zuciya nesa, kuma ba ta da niyyar kara ta’azzara lamarin.
A nasa bangaren kuwa, Wang ya ce, kasar Sin na matukar yin Allah wadai da kakkausar murya kan harin da aka kai kan sashin karamin ofishin jakadancin Iran da ke Damascus, tare da mai da shi a matsayin babban cin zarafin dokokin kasa da kasa, kuma ba za a amince da hakan ba.
Kasar Sin ta lura da furucin na Iran na cewa matakin da ta dauka yana da iyaka, kuma wani mataki ne na kariyar kai a matsayin martani ga harin da aka kai kan karamin ofishin jakadancin Iran a Syria, a cewar Wang.
Ya kara da cewa, an yi imanin cewa Iran za ta iya tafiyar da lamarin yadda ya kamata, tare da kiyaye zaman lafiya a yankin da kare ikonta da martabarta.
A wannan rana, Wang Yi ya kuma yi tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na kasar Saudiyya Faisal bin Farhan Al Saud, game da halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya, da kuma alakar Sin da Saudiyya. (Mai Fassarawa: Yahaya Mohammed)