Kura ta tirnike fagen siyasar Jihar Kano a wannan makon sakamakon sanarwar dakatar da shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje daga mazabarsa da ke Dawakin Tofa.
Duk da cewa har yanzu tsugune ba ta kare ba dangane wannan batu duk da sanarwar dakatar da wadanda suka aiwatar da abin daga shugabannin jam’iyya na karamar hukumar da Ganduje ya fito, ana ganin wani babban tarko ne da aka dana wa shugaban jam’iyyar a Kano.
- Sin Na Tsayawa Kan Goyon Bayan Falasdinu Don Zama Mamba A Hukumance A MDD
- Jihar Benuwai Ta Bankado Mutum 35 Masu Yi Wa Sirin Tattara Harajinta Zagon-Kasa
Hakazalika, gurfanar da shi a gaban shari’a a gaban Babbar Kotun Jihar Kano bisa tuhumar da ake yi masa na cin hanci da rashawa tare da uwargidansa da dansa ma wani tarko.
A cewar bayanan kotun, ana tuhumar Ganduje da matarsa, Hafsat da dansa, Umar da kuma wasu mutum biyar kan aikata laifuka 8 da suka hada da cin hancin kudi na Dala 413,000 da kuma Naira biliyan 1.38.
Gwamnatin jihar ta ce tana da shaidu 15 wadanda za su bayar da shaida a gaban kotu.
Gwamna Abba ya zargi Ganduje da wawushe kudaden al’ummar Jihar Kano da kuma filaye wanda ya mallaka wa iyalansa.
Wannan ba sabon abu ba ne na zargin shugaban jam’iyyar APC na kasa da iyalansa kan cin hanci da rashawa.
Zargin ya samo asali ne tun wani bidiyon da ya nuna Ganduje na amsar dala yana zubawa a aljihunsa, wanda aka yi zargin ya amsa cin hanci ne daga wurin ‘yan kwangila da Editan jaridar Daily Nigerian, Jafar Jafar ya fitar a watan Oktoban 2018.
An dai boye fuskar wanda aka yi ikirarin dan kwangila ne a cikin bidiyon lokacin da yake bai wa Ganduje kudaden, sai dai kawai aka nuna hannunsa.
Masu sukarsa sun yi tunanin wannan bidiyon zai hana Ganduje samun mulki wa’adi na biyu, amma duk haka a ranar 31 ga Janairun 2019, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya goyi bayansa duk da zargin da ake yi masa.
Ganduje ya musanta cewa shi ne a wannan bidiyon ta bakin tsohon kwamishinansa, Malam Muhammad Garba, inda ya yi ikirarin cewa an hada bidiyon ne domin a bata masa suna.
An dai yi ta gwagwarmaya kan wannan bidiyo wanda ta kai har da shiga kotu domin tabbatar da gaskiyar labari. Lamarin da ta kai wata babbar kotun Jihar Kano ta hana majalisar dokokin jihar biciken Ganduje kan wannan zargi.
Haka kuma, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano ta sake bankado sabon laifin cin hanci da rashawa da take tuhumar Ganduje.
Shugaban hukumar, Muhuyi Magaji, ya bayyana hakan a lokacin wani tattaunawa da gidan talabijin na Channels a ranar Talata, inda ya zargi gwamnatin Ganduje da wawushe kudaden al’umma ba bisa ka’ida ba.
Ya ce bincike ya nuna cewa an kwashe kudin kananan hukumomi da suka kai naira biliyan 51.3 ba tare da sanin hukumomi ba.
A cewar Magaji, a duk wata sai gwamnatin Ganduje ta kashe naira biliyan 1 daga asusun jihar ba bisa ka’ida ba. Sannan ya yi ikirarib cewa tura naira biliyan 4 a cikin asusun wani kamfanin noma daga kudaden harajin Jihar Kano ba tare da wani dalili ba.
Ya ce sun shigar da dukkan wadannan tuhume-tuhumen a gaban kotu.
Haka kuma a watan Yulin 2021, iyalan Ganduje sun kara fuskantar zargin cin hanci da rashawa bayan da dansa, Abdulzeez Ganduje ya shigar da mahaifiyarsa, Hafsat kara.
Abdulzeez ya tuhumi mahaifiyarsa da mallakar kadara ba bisa ka’ida a lokacin da ta yi amfani da karfin ikon da take da shi.
Hukumar EFCC ta yi wa matar gwamnan tambayoyi na sa’o’i biyar a watan Oktoban 2021 bisa wannan zargi.
Daga bisa gwamnatin jihar ya musanta kama matar gwamnan, inda ta siffanta lamarin da jita-jita daga wurin ‘yan adawa.
Ana tunanin cewa tun lokacin da aka zabi Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa, an kashe dukkan zargi da ake masa na cin hanci da rashawa.
Amma sai gashi a ‘yan kwanakin nan, Gwamna Abba ya bukaci hukumar EFCC ta fitar da sakamakon binciken bidiyon dala.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna, Sanusi Tofa ya fitar, ya bukaci Ganduje ya shirya fuskantar shari’a maimakon magana kan gazawar gwamnati mai ci.
A nasa martanin, Ganduje ya zargi Gwamna Abba da fito da wannan lamarin ne domin dauke hankali kan gazawar gwamnatinsa na kasa yi wa mutanen jihar aiki.
A wata sanarwa da ya fitar, babban sakataren yada labarai na shugaban jam’iyyar APC, Edwin Olofu ya bayyana cewa wannan kokarin gwamna ne na boye gaskiyar lamari kasancewa ya kasa gudanar wa jama’a ayyukan da suka kamata tun lokacin da ya hau karagar mulki.
A matsayinsa na shugaban jam’iyyar APC na kasa, mutane da dama sun tabbatar da cewa EFCC ko wata hukuma karkashin gwamnatin tarayya ba za su iya kama Ganduje da laifin da ake zargin ya aikata ba, saboda yadda yake da goyon bayan gwamnatin tarayya.
A watan Yunin 2022, Gwamnan Jihar Ribas karkashin jagorancin tsohon gwamna, Nyeson Wike ya gaza samun nasara kan zargin da ya yi wa tsohon gwamnann da ya gada, Rotimi Amaechi, a lokacin yana ministan sufuri, kan zargin handame naira biliyan 96 wajen sayar da kadarorin jihar.
A watan Mayun 2022, kotun koli ya yi watsi da binciken tuhumar da gwamnatin Wike ke yi wa Amaech.
Sai dai a watan Oktobar 2022, gwamnatin jihar ta janye tuhumar da take yi wa Amaech da wasu mutum shida.
Abubuwan da suka faru a baya sun nuna cewa hukumomin gwamnatin tarayya ne kadai za su iya tuhumar tsohon gwamna kan zargin cin hanci da rashawa.
Yanzu dai ana jiran a ga ko Gwamna Abba zai iya samun nasara kan tuhumar da yake yi wa Ganduje, bisa yadda yake da goyon bayan gwamnatin tarayya.
Wasu na ganin Gwamna Abba zai iya yin nasara, tun da har shugabannin jam’iyyar APC a mazabar Ganduje na karamar hukumar Dawakin Tofa sun sanar da dakatar da shi.
Mai bai wa jam’iyyar shawara kan harkokin shari’a a mazabar Ganduje, Hon. Halliru Gwanzo ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano.
Halliru Gwanzo ya ce sun yanke shawarar dakatar da Ganduje daga jam’iyyar ne sakamakon zarge-zargen da Gwamnatin Jihar Kano ta yi masa na karbar cin hanci.
Sun ce dakatarwar ta fara ne daga ranar 15 ga Afrilu.
Sai dai kuma daga bisani, kwamitin ayyuka na jam’iyyar APC reshen Jihar Kano ya sanar da dakatar da wasu jiga-jigan jam’iyyar a unguwar Ganduje da ke karamar hukumar Dawakin Tofa ta jihar, wadanda a baya suka sanar da dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa daga jam’iyyar.
Wannan wani martani da shugabannin jam’iyyar na karamar hukumar suka yi cikin gaggawa, sun yi watsi da dakatarwar tare da korar wadanda ke da hannu wajen dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa.
Shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Dawakin Tofa, Inusa Suleiman Dawanau, ya shaida wa manema labarai a Kano a ranar Litinin cewa, wadanda ke da hannu a dakatar da shugaban jam’iyyar APC na kasa, sun shiga cikin bata-gari ne ta hanyar yin zagon kasa ga jam’iyyar APC tare
da hadin kai ga jam’iyya mai mulki a jihar.
Baya ga dakatarwar, kwamitin ayyuka na jam’iyyar a matakin jiha, ya kuma sanya wa shugabannin jam’iyyar a unguwar Ganduje takunkumi na tsawon watanni shida tare da kafa kwamitin bincike na musamman domin tabbatar da wasu zarge-zarge da ake yi musu.
Sai dai kuma, zuwa lokacin rubuta wannan labarin, mun samu rahoton cewa Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta tabbatar da sahihancin dakatarwar da aka yi wa Ganduje, amma da yiwuwar zai iya daukaka kara.