Da alama har yanzu tsugune ba ta kare ba a tsakanin tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello da Hukumar Yaki da Karya Tattalin Arzikin Kasa da Zamba ta EFCC, inda shugaban hukumar, Ola Olukoyede ya yi barazanar cewa zai yi murabus matukar ba a hukunta tsohon gwamnan ba.
Mista Ola ya fadi hakan ne a wani taron manema labarai a shalkwatar EFCC da ke Abuja, a ranar Talata tare da jaddada cewa hatta wadanda suka bai wa Yahaya Bello mafaka su ma za su fuskanci fushin doka.
- Sarkin Kano Ya Shawarci Ministan Sadarwa Kan Amfani Da Fasaha
- Hajji: Saudiyya Ta Gargadi Kamfanonin Bogi Kan Aikata Damfara, Ta Jadadda Muhimmancin Biza Ga Mahajjata
A farkon makon nan, tsohon gwamnan, Yahaya Bello ya bayyana cewa a shirye yake ya gurfana a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja domin amsa tambayoyi kan tuhume-tuhumen da hukumar kula da cin hanci da rashawa (EFCC) take yi masa har guda 19, amma yana tsoron ya fito ne a cafke shi.
Yahaya Bello bai gurfana a gaban kotu na zaman shari’ar ba a ranar Talata, ya yi magana ne ta bakin tawagar lauyoyinsa a madadinsa.
Daya daga cikin tawagar lauyoyinsa, Mista Adeola Adedipe ya bayyana wa alkali cewa wanda yake karewa baya tsoron gurfana a gaban kotu, amma yana mutukar tsoron a kama shi.
“Wanda ake uhuma yana son zuwa kotu, amma yana tsoron umurnin da aka bayar da kama sh,” in ji Adedipe.
Saboda haka, ya bukaci kotu ta janye umurnin kama da aka bayar tun da farko. Adedipe ce kamar yadda aka bayar da umurnin a kama shi, hakan ya saba wa doka na kare wanda ake tuhuma.
Ya ce a lokacin wannan zaman shari’ar na ranar Talata ne kadai kotu ta amince a mika karar da ake wa wanda ake tuhuma wurin lauyansa domin kare shi.
Sai dai kuma tsahon gwammann ya yi ikirarin cewa EFCC haramtacciyar hukuma ce.
A cewarsa, gwamnatin tarayya ba ta shawarci dukkan jihohi 36 da ke kasarr nan kafin kafa dokokin EFCC ba ta hanyar majalisar kasa.
Ya ce sashi na 12 na kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999, wanda aka yi wa kwaskwarima, ya bukaci majalisun dokoki da ke jihohi su amince da wani doka kafin a fara aiwatarwa.
“Wannan batu yana da matukar muhimmanci game da tsarin mulkin kasa da dokokin tarayya. Ya kamata a warware shi kafin EFCC ta zama halartacciyar hukuma,” in ji lauyan Yahaya Bello.
Sai dai kuma lauyan Hukumar EFCC, Mista Kemi Pinheiro, ya bukaci kotu a kan karta amince da bukatar lauya mai kare wanda ake tuhuma. Ya ce bai kamata a kyale batun kama shi ba har sai wanda ake kara ya mika kansa a gaban kuliya.
Lauyan EFCC ya kara da cewa sashe na 396 na dokar kasar nan ya tanadi cewa, kotu ba ta da hurumin amsar duk wani bukata na wanda ake kara har sai ya mika kansa a gaban kotu.
Ya ce hukumar ba za ta janye batun kama shi ba har sai wanda ake tuhuma ya mika kansa a zama na gaba da kotun za ta yi. Ya ce tuhumar da ake masa ba ta da alaka da jiha ko majalisa, tuhuma ce a tsakanin wani mtum ake yi masa zargin yin almundahana da kudaden jama’a.