Dan takarar gwamnan jihar Zamfara a karkashin jam’iyyar PDP, Dr. Dauda Lawal ya taya zababben gwamnan jihar Osun, Adeleke Nurudeen Ademola murnar nasarar da ya samu a zaben gwamnan jihar Osun da aka kammala.
Jami’in zaben Gwamnan jihar Osun na Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, Farfesa Oluwatoyin Ogundipe a safiyar ranar Lahadi, ya bayyana Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben. Tsohon Sanatan ya zama wanda ya lashe zaben gwamnan ne da kuri’u 403,371.
Lawal a cikin sakon taya murnar da ofishinsa na yada labarai ya fitar a Gusau, babban birnin jihar Zamfara ya ce yana da yakinin Adeleke zai iya aiwatar da abin da al’ummar jihar Osun ke bukata.
Ya ce nasarar da aka samu wata alama ce da ke nuna cewa al’ummar Jihar Osun da ma Nijeriya baki daya har yanzu suna da kwarin guiwar cewa jam’iyyar PDP za ta iya samar da kyakkyawan shugabanci da kuma yi wa jama’a hidima mai inganci. Ya bayyana Adeleke a matsayin mutumin da ya dace inda ya ce ko shakka babu zai yi kyakkyawan shugabanci idan aka rantsar da shi a ofis.
“Mutanen Osun sun yi zaben da ya dace ta hanyar zaben Sen. Adeleke na PDP. Zan iya tabbatar wa da mutanen Osun cewa PDP da zababben gwamnan suna da duk abin da ya kamata domin share muku hawaye da samar muku da hanyar ribatar dimokuradiyyar da ta kubuce muku.
“Tare da Sen. Adeleke a kan kujerar mulki, ba na shakkar cewa nan ba da jimawa ba jihar za ta samu ci gaba mara misaltuwa ta fuskacin zamantakewa, tattalin arziki da kuma siyasa”, inji shi.
Dan takarar Gwamnan na PDP na Zamfara ya kuma yaba wa Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, kungiyoyin fararen hula, da Jami’an tsaro na ganin cewa zabin da al’umma suka yi ya yi nasara a jihar ta Osun.