Gwamnonin Arewa sun bayyana kwarin gwiwarsu na cewa tare da goyon baya da hadin kai za su shawo kan duk wani kalubale kuma za su cimma burinsu na samar da makoma mai kyau ga yankin Arewa da Nijeriya baki daya.
Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Gombe, Alhaji Mohammadu Inuwa Yahaya ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a taron kungiyar da ya gudana a ranar Talata a gidan gwamnati a Kaduna.
- NNPCL Ya Bayyana Ranar Da Matatar Man Fetur Ta Kaduna Za Ta Fara Aiki
- Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yan Bindiga Sun Sake Kutsawa Garin Abuja, Sun Sace Mutane 4
Alhaji Yahaya ya ce, gina dan Adam na da matukar muhimmanci ga ci gaban yankin, inda ya koka da cewa, a halin yanzu, Arewacin Nijeriya ne ke da mafi yawancin yaran da ba sa zuwa makaranta a duniya.
Gwamnan ya bayyana hakan da dewa, sam bai dace ba kuma dole ne a yi gaggawar magance wannan matsala, wanda ya ce, kowane yaro ya cancanci samun ingantaccen ilimi da kuma damar bunkasa fasahar da ake bukata don samun nasara.
Ya kara da cewa, bangaren tsaro yana kan gaba a abubuwan da kungiyar ta fifita, yana mai jaddada cewa, a taron da suka yi na karshe, kungiyar ta jaddada aniyarta na yin aiki tare da gwamnatin tarayya, domin samar da mafita mai dorewa kan kalubalen tsaro dake addabar yankin.
A nasa jawabin, gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya bayyana cewa, taron ya ba su damar duba nasarori da kalubalen da suka samu kawo yanzu a yakin da ake da ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da kuma kirkiro sabbin dabarun tunkarar wadannan makiya masu hana ci gaba.
Gwamna Sani ya sake nanata kiransa na tun farko ga kungiyar da su samar da dabaru da tsare-tsare na bai daya don magance matsalar rashin tsaro ta hanyar kafa Cibiyar Gudanarwa don daidaita ayyukan kungiyar na hadin gwiwa.
Ya bukaci takwarorinsa da su sake bullo da dabara domin cimma matsaya kan samar da tsarin bai daya na ci gaban Arewacin Nijeriya.
Daga cikin mahalarta taron, akwai Gwamnonin Bauchi, Zamfara, Katsina, Kaduna, Nasarawa, Gombe, Maiduguri yayin da Jigawa, Kano, Filato, yobe, Benuwe, Kwara, Neja, Adamawa da Sokoto, suka turo mataimakansu.