Wasu dillalan gidaje a Hotoro (GRA) a jihar Kano sun danganta tashin farashin fili a yankin da kafuwar jami’ar Maryam Abacha (MAAUN) da ke Kwanar Maggi a yankin.
Daya daga cikin dillalan a yankin, Muhammad Najume, ya shaida wa wakilinmu cewa, tashin farashin ya fara ne nan take bayan da aka fara gudanar da harkokin karatu a jami’ar.
- Kotu Ta Kulle Wani Malami Kan Zargin Fyaɗe A Legas
- Champions League: Bayern Munich Da Real Madrid Sun Tashi Canjaras
Najume ya bayyana cewa, filin da aka sayar da shi kan Naira miliyan 20 a shekarar 2023 a yanzu ana sayar da shi a kan kusan Naira miliyan 150 ko sama da haka.
“Wannan za a iya danganta shi da yanayin tattalin arziki da kasancewar jami’ar a yankin.
Ya kara da cewa, “Tashin farashin ba wai kawai ya shafi yankin Hotoro ba ne, har ya kai ga makwabtan yankin”.
Wani Dillali, Mallam Isa, ya kara bayyana cewa, gidan da bai wuce Naira 500,000 a cikin shekaru uku da suka gabata ba, yanzu ya kai kusan Naira Miliyan 3.