A bayyana yake cewa,Israi’la da HAMAS na yaki a tsakaninsu inda Amurka ke goyon bayan kasar Isra’ila yayin da kuma kasar Iran ke goyon bayan kungiyar HAMAS ta wani bangaren.Wannan na kara bayyana ne in aka lura da hare-haren da Iran ta kaddamar a kan yankin Isra’ila da makamai ta hanyar amfani da jirage marasa matuka da aka fi sani da suna DRONE. Amurka da Birtaniya suka jagoranci kakkabo wasu daga cikin makaman da Iran ta harba wa Isra’ila.Wannan kuma yana zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ke shirin mayar da martani a kan barazanar ta kasar Iran ga al’ummar kasarta. Ra’ayoyi daga kasashen duniya na nuna damuwa a kan yadda barazanar yakin take kara karuwa a yankin gabas ta tsakiya, musamman ma ganin yadda manyan kasashen duniya ke kara kasafin-kudinsu na bangaren samar da kayan yaki ga dakarunsu.Mun yi rubutu a kan wannan lamarin a watan Janairu, mun sake dawo da shi ne a yanzu saboda ganin yadda yiyuwar aukuwar yakin duniya na uku take kara kankama a ‘yan kwanakin nan.
Abubuwan da suke faruwa a sassan duniya na kara karfafa tsoron da ake yi na yadda kasashen duniya ke wasa da bubuwan da za su iya haifar da yakin duniya na uku.
- Kwamitin Sulhun MDD Ya Kira Taron Gaggawa Kan Yanayin Da Palastinu Da Isra’ila Ke Ciki
- Sin Ta Raba Basira Da Karfinta Na Inganta Warware Rikicin Ukraine Ta Hanyar Siyasa
Yakin duniya da aka yi na karshe wanda shi ne yakin duniya na biyu, wanda aka kawo karshensa a shekarar 1945.Har zuwa yanzu duniya na alhinin barnar da matsalolin da yakin ya haifar wa rayuwuar al’ummar duniya.Yakin da aka fara a shekarar 1939, yana nan a zukatan al’umma har zuwa wannan lokacin.An lalata yankin nahiyar Turai.Kasar Japan ta dandana kudarta a radadin makaman Nukiliya. Kasar Amurka ta dandana radadin yakin ne a yankin gabar tekun Pearl lokacin da kasar Japan ta kai wa dakarunta hari a shekarar 1941,hakan na daga cikin manyan dalilan da suka sanya Amurka ta shiga yakin gadan-gadan.Har zuwa yanzu kasar Jamus na rayuwa da kunyar da ta sha sakamakion kayen da shugabanta na wancan lokacin Adolf Hitler ya sha.Bayan kawo karshen yakin yankin da tarayyar Turai ta shiga bukatar tsari na musamman don sake gina yankin bayan tarwatsa shi da aka yi.
An kafa Majalisar Dinkin Duniya ne domin ta tabbatar da kawo karshen duk wata matsalar da za ta iya haifar da yaki a tsakanin kasashen duniya,amma kamar takwararta ta baya ‘League of Nations’ wadda aka kafa bayan kawo karshen yakin duniya na 1 (1918)ta kasa maganin matsalolin da za su iya haifar da yaki a tsakanin kasashen duniya.
A karkashin jagorancin kungiyar samar da zaman lafiya a duniya, sai gashi ana buga gangar yaki amma kuma ta kasa yin wani abin da zai iya dakile yiyuwar aukuwar yakin. Abin takaici a nan shi ne yadda a halin yanzu Majalisar Dinkin Duniya ta rasa mutuncin ta,ta yadda har mambobinta ba su saurara mata a kan duk wani kudurin da ta zartar. A halin yanzu taron Majalisar Dinkin duniya ya zama fage ne na surutu, sannan duk wata shawarar da aka zartar bata da wani tasiri, babu wata kasar da za ta mutunta yarjejeniyar ko kuma amfanin da ita, abin ya zama tamkar taron shan shayi ne.
Muna cikin damuwa, musamman ma in har aka samu aukuwar yakin duniya na uku, irin makaman da za a shigo da su za su zama makamai ne masu matukar barna (WMD) wadanda za su iya haifar da mace-mace masu yawa.Tsoron kuma shi ne, irin makaman da aka yi mamfani da su a lokuttan yakin duniya na 1 da na biyu suna iya zama tamkar wasan yara.Akwai yiyuwar a yi amfani da muggan makamai in har aka samu aukuwar yakin duniya na uku, musamman ma ganin yadda manyan kasashe kamar Rasha da Amurka suke nuwa wa junansu yatsa, kuma gashi wadannan kasashe na kokarin jawo kasashen Koriyan ta Arewa da Iran a cikin yakin.Kasashen na neman suma a karbe su a mastayin kasashe masu karfin makaman yaki.
A kan haka ne hankalin wannan jaridar ya tashi a kan yiwuwar aukuwar yakin duniya na uku, domin haka ne muke kira ga kasashen duniya su yi kokarin kauce wa dukkan abubuwan da za su kai ga sa yakin duniya na uku musamman ganin irin matsalar da al’ummar duiniya za su shiga na wahalhalu da rashe-rashen rayuwaka.Muna wannan kiran ne musamman ganin idan yakin ya auku, al’umma ne kawai za su dandana ba tare da nuna banbanci ba.
Idan muka duba yadda al’amuran ke tafiya a sassan duniya, musamman sakamakon talauci a tsakanin kasashe, yadda mutane ke gudun hijira sakamakon yake-yake na cikin gida,da yadda mutane ke barin garuruwansu don neman ayyukan yi a wasu kasashe, duk wadannan ya kamata su zama mana darasi na tabbatar da an kaucewa yiyuwar aukuwaer yaki a duniya.
A halin yanzu kasashen Rasha da Yukrain na can suna fafatawa a tsakaninsu a yakin da masana suka yi ma kwatance da yaki mai sarkakakiya,kasashen da ke makwabtaka da su na nan na dandanawa sakamakon turuwan ‘yan gudun hijira da sauran matsalolin da yakin ya haifar.Irin wannan kuma yana ruruwa a tsakanin Isra’ila da HAMAS inda Amurka da Iran suke yayyafa wa lamarin fetur.
Babban rikicin da za a iya fuskanata in har aka samu aukuwa yakin duniya na uku shi ne yadda yawancin kasashen da ke yi wa junansu kallon hadarin kaji duk sun mallaki makaman nukiliya, wannan ne ma shugaban hukumar kula da makaman nukiliya na duniya (IAEA),Rafael Mariano Grossi, ya yi gargadin cewa, lallai duniya na wasa da wuta in har ba a tsabbatar da dakatar yiwuwar aukuwar yakin duniya na uku ba.
Ra’ayin wannan jaridar shi ne, lallai lokaci ya yi da duniya za ta rungumi tattaunawa waje warware dukkan rikice-rikicen da ke tasowa a tsakanin kasashe.Tattaunawa ta fi fuskantar juna da yaki. Muna kira gare su dauki matakin gaggawa na ganin ba a samu aukuwar yakin duniya na uku ba.