Ranar 4 ga watan Mayu rana ce ta matasa a kasar Sin. Hausawa su kan ce, matasa su ne manyan gobe. Sai dai duk da haka, matasa na fuskantar matsin lamba a fannonin neman damar karatu, da guraben aikin yi. Ta yaya matasa za su iya raya kansu, gami da zama masu daukar nauyin raya kasa?
Akwai wani karin magana na Sinawa dake cewa, “yanayin zamani shi ke haifar da jarumai”. Ma’anarsa ita ce, tafiya tare da zamani, zai sa mutum samun cikakkiyar damar raya kansa. A ganina, wannan magana na da ma’ana. Ko a fannin raya harkokin matasa ma, kamar haka yake. Ya kamata a yi amfani da damammakin da zamani ya samar, musamman ma wadanda kokarin gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya ta Sin da Afirka ya haifar.
- Ministan Wajen Hungary Na Fatan Ziyarar Xi Za Ta Bude Sabon Babi Na Dangantakar Hungary Da Sin
- Jigon Baje Kolin Al’adun Sin “Gamuwa Da Sin” Ya Bayyana A Baje Kolin Kasa Da Kasa A Paris
Ci gaban harkokin matasa na bukatar bunkasar sana’o’i. A wannan fanni, hadin gwiwar Sin da Afirka na taka muhimmiyar rawa.
Cikin shekarun nan, aikin zuba jari ga kasashen Afirka na kasar Sin na samun ci gaba yadda ake bukata. Inda yawan kudin da Sin take zubawa kai tsaye a fannin samar da kayayyaki a kasashen Afirka, ya kai fiye da dalar Amurka miliyan 400 a duk shekara. Kana darajar hadin kan bangarorin Afirka da Sin ta fuskar gina kayayyakin more rayuwa, ta kai fiye da dala biliyan 37 a duk shekara. Hadin gwiwar bangarorin 2 ya shafi zirga-zirgar ababen hawa, da aikin gona, da makamashi, da tattalin arziki mai alaka da fasahohin zamani, da fasahohin bunkasa tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba, da dai sauransu, ta yadda ya taimaki kokarin raya masana’antu da habaka tsarin tattalin arziki zuwa fannoni daban daban a kasashen Afirka, da samar da dimbin guraben aikin yi, gami da damammakin raya sana’o’i ga matasan kasashen.
Ban da haka, ci gaban harkokin matasa ba zai rasa alaka da karuwar ilimi da ingantuwar fasahohi ba, inda a wannan fanni ma hadin gwiwar Sin da Afirka ya samar da goyon baya sosai.
A shekarar 2018, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da wasu muhimman matakai 8 a fannin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, a wajen taron koli na Beijing na dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka, matakan sun kunshi horar da kwararrun masana matasa masu ilimin aikin gona da masu jagorantar aikin wadatar da manoma ta wasu sabbin fasahohi a kasashen Afirka, da samar da damammakin samun horon fasahohin sana’o’i ga matasan Afirka, da taimakon kafa cibiyoyin bude sabbin kamfanoni da kirkiro sabbin fasahohi na matasa, da gayyatar matasan Afirka 2000 domin ziyarar kasar Sin, da dai sauransu. Kana a lokacin da shugaban ya halarci taron musayar ra’ayi na shugabannin kasashen Afirka da Sin, da ya gudana a kasar Afirka ta Kudu a bara, ya yi karin alkawuran da suka shafi horar da wasu ma’aikata masu fasahohin sana’o’i gami da iya yaren Sinanci dubu 10 a duk shekara a kasashen Afirka, da kulla huldar hadin kai tsakanin jami’o’i dari 1 na kasashen Afirka da kasar Sin, da dai makamantansu. Wadannan matakai na nufin taimakawa matasan Afirka samun sabbin ilimi da fasahohi, ta yadda za su iya raya kansu yadda suke bukata.
Cikin shekaru 20 da suka wuce, na gamu da matasan kasashen Afirka da yawa, wadanda suka kulla wata alaka da kasar Sin. Wasunsu na karatu a kasar Sin, wasu suna aiki a kamfanonin kasar Sin dake kasashen Afirka, yayin da kuma wasunsu ke gudanar da ciniki tsakanin bangarorin Sin da Afirka, kuma dukkansu sun samu ci gaba sosai a harkokinsu.
A shekarar da ta gabata na gamu da wata daliba ‘yar Najeriya a garin Jinhua dake gabashin kasar Sin, wadda ta taba koyon Sinanci a wata kwalejin Confusious dake Najeriya, sa’an nan ta samu kudin tallafin don ta yi karatu a kasar Sin. Yanzu tana neman ci gaba da karatun digiri na 2 a kasar. Haka kuma, na tuna da wani saurayi dan jihar Kano ta Najeriya, wanda na gamu da shi a birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin wasu shekaru da suka wuce. A lokacin yana zaune a birnin Guangzhou, inda yake sayen kayayyakin wayar salula, yana tura su zuwa Najeriya a kai a kai. Ko da yake shekarunsa 20 da wani abu ne kacal a lokacin, amma ya riga ya mallaki wasu shagunan sayar da wayar salula guda 3 a wasu kasuwannin dake Kano.
Wadannan matasa da suka taba hulda da kasar Sin suna girmama zumuntar dake tsakanin Afirka da Sin. Saboda sun fahimci cewa, zumunta mai zurfi da hadin gwiwar da ake samu tsakanin Afirka da Sin, na ba su damar raya harkokinsu cikin nasara.
Sande Ngalande, darakta ne na cibiyar nazarin batutuwa masu alaka da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” ta jami’ar Zambia. Ya taba bayyana cewa, dabarar kasar Sin ta zamanantar da kasa ta amfani kasashen Afirka, inda dimbin matasan Afirka masu sana’o’i daban daban ke son mu’ammala da Sin, da fahimtar Sin, da koyon fasahohin kasar Sin. Kana ta hanyar hadin gwiwar Sin da Afirka, matasan Afirka suna iya kulla zumunci mai zurfi da Sinawa, gami da samun damar raya kansu, da kasashensu, gami da tabbatar da ci gaba mai dorewa a nahiyar Afirka.
Cikin shirin ajandar shekarar 2063 na kungiyar kasashen Afirka ta AU, an ce ya kamata a sanya matasa su zama karfin farfado da nahiyar Afirka, kuma hadin gwiwar Sin da Afirka na taimakawa wajen ganin tabbatuwar wannan buri a zahiri. (Bello Wang)