Hukumar kula da wutar lantarki ta kasa (NERC), ta umarci kamfanin samar da wutar lantarki da ya rage yawan wutar da ake bai wa abokan hulda a kasashen ketare domin bunkasa samar da wutar lantarki a cikin gida.
Wannan na cikin wani umarni da ta fitar a ranar Juma’ar da ta gabata, NERC ta ce tsarin da kamfanin samar da wutar lantarki ke bi a halin yanzu ya jawo wa ‘yan kasar wahalhalu.
- Kalubalen Koyarwa: Hukumar UBEC Ta Kaddamar Da Horas Da Malamai 1,480 Da Ke Makarantun Karkara
- Yanzu-yanzu: Shettima Ya Dakatar Da Tafiyarsa Zuwa Amurka Saboda Matsalar Jirgi
Hukumar daidaita rabon wutar ta ce ta sanya kashi shifa a kan wutar da za a samar ga kasa da kasa na tsawon watanni shida masu zuwa.
Kamfanonin samar da wutar lantarki a Nijeriya na da kwangiloli da kasashen Afirka da ke makwabtaka da su don samar da makamashi.
Hakan na tallafa musu da kudaden shiga daga harajin tattalin arziki, duk da haka, wadannan kamfanoni ba ko yaushe su ke biya a kan lokaci ba.
Ana yawan samun katsewar wutar lantarki a Nijeriya saboda karancin wutar lantarki amma abin ya kara kamari a baya-bayan nan.
Idan ba a manta ba an yi wa kwastomomin da ke tsarin Band A karin kudin wutar lantarki wanda za su rika samun wutar lantarki a kullum, ko sa’o’i 20.
Sai dai karin ya bar baya da kura, inda mutane da dama suka dinga kira da a janye karin, a gefe guda kuma masu ruwa da tsaki suka bayyana cewar karin bai zo a lokacin da ya dace ba, duba da irin halin matsin tattalin arziki da ake fuskanta a Nijeriya.