A yayin da ‘yan Nijeriya ke ci gaba da kokawa a kan rashin saukar farashin kayayyaki, Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Tabbatar da Zaman Lafiya da Wayar da Kai ta Kasa (NACOPEAM), Dakta Ahmad Saleh, ya bayyana hanyoyin da za a bi; don warware matsalar hauhuwar farashin kaya a Nijeriya.
Saleh ya bayyana abubuwan ne a shirin Barka Da Hantsi Nijeriya na Sashen Talabijin na Intanet na LEADERSHIP Hausa, da aka gabatar ranar Larabar da ta gabata.
- Almundahana: Kotu Ta Bayar Da Belin Hadi Sirika Da ‘Yarsa
- Majalisar Wakilai Ta Umarci CBN Ya Dakatar Da Harajin Tsaron Yanar Gizo
Dakta Saleh, ya nunar da cewa matukar ana so a cimma burin haka, da farko ya kamata a kafa Hukumar Kayyade Farashi a Nijeriya.
“Idan ana so farashin kaya ya sauka a wannan kasa, wajibi ne a kafa wannan hukuma; wadda za ta yi aiki a lungu da sako na wannan kasa baki-daya.”
Kamar yadda Daktan ya bayyana a shirin, ya ce kafa wannan hukuma zai taimaka wajen kayyade farashin kayayyaki, inda ya bayar da misali da cewa ana sayar da Simintin Dangode a kan dubu shida da wani abu a Legas amma a Mambila Naira dubu tara ake sayarwa kuma a cikin kasa daya wanda haka bai kamata ba.
Haka zalika, dole ne wannan hukuma ta tabbatar da samar da farashin bai-daya a dukkanin kananan hukumomi 774 da muke da su a Nijeriya. “Wannan na daya daga cikin abubuwan da za su taimakawa wajen saukar farashin kayayyakin da ke ci wa ‘yan Nijeriya tiwo a kwarya a daidai wannan lokaci.” Ya bayyana.
Abu na biyu, kamar yadda Dr. Saleh ya bayyana shi ne, Bunkasa Masana’antun Cikin Gida: Bunkasa masana’antu zai taimaka kwarai da gaske wajen saukar farashin kayayyaki a cewar Masanin, domin kuwa a duk yayin da ya kasance abubuwan da ake shigowa da su; sun rinjayi wadanda ake fita da su, dole ne a fuskanci matsalar hauhawar farashin kaya.
Ya kara da cewa, wajibi ne gwamnati ta mayar da hankali wajen farfado da masana’antu tare da karfafa samar da abubuwan da za a rika fitar da su zuwa kasashen ketare, don sake farfado da tattalin arzikin wannan kasa, misali kamar bangaren harkar noma, ma’adanai da sauran makamantansu.
Domin kuwa, Nijeriya kasa ce da Allah ya azurta da dukkanin wani nau’i na arziki, wanda idan aka tsaya aka kyautata amfani da shi yadda ya kamata, za a samu kyautatuwar tattalin arziki da wadata da kuma jin dadi a kasar baki-daya.
Sai kuma na uku, da ya yi kiran a kafa Kotun Hukunta Duk Wanda Ya Bijire Wa Dokar Kasa: “Idan har ana so a cimma wannan manufa ta samun saukar farashin kayayyaki a fadin wannan kasa, ya zama wajibi ya kasance ana hukunta duk wanda ya ci karo da doka. Misali, a Kasar Ghana, lokacin da bankuna suka saba wa ka’idojin harkokin kudaden waje; ba tare da wani bata lokaci ba aka hukunta su”, in ji Daktan.
Don haka, ya zama dole Nijeriya ta mike tsaye wajen hukunta masu aikata laifuka, musamman ma wadanda aka samu da laifin cin hanci da rashawa, ya kasance ana yanke musu hukunci irin na babu sani; babu sabo. Dalili kuwa, babu abin da ya mayar da Nijeriya baya tare da dakile ci gabanta, kamar wannan dambarwa ta cin hanci da rashawa a wannan kasa, a cewar Dakta Sale.