Jam’iyyar PRP ta bi sahun ‘yan Nijeriya wajen gargadin gwamnatin tarayya kan gayyato sojojin Amurka da wasu sauran kasashen Turai domin su kafa sansanoninsu na soja a Nijeriya.
A cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar tare da sa hannun mukaddashin sakataren yada labaranta na kasa, Kwamared Muhammed Ishak, ta ce barin sojojin kasashen waje su shigo Nijeriya bayan an kore su daga wasu kasashe kamar irinsu Senegal da Nigarr babban hatsari ne ga tsaron kasa da kuma lafiyar ‘yan Nijeriya.
- CBN Ya Bayyana Sunayen Bankuna 41 Da Ya Aminta Da Ingancinsu A Nijeriya
- Sinawa Ba Za Su Manta Da Danyen Laifin NATO Na Kai Wa Yugoslavia Hari Ba
Jam’iyyar ta bukaci gwamnatin tarayya ta yi watsi da irin wannnan tunani domin bai dace da manufar kasa ba, saboda baraza ce ga ‘yancin Nijeriya da tattalin arziki da difilomasiyya na tusa manufar kasashen waje cikin kasa mai ‘yancin gashin kai kamar Nijeriya.
“Jam’iyyar PRP ta bi sahun ‘yan Nijeriya wajen jawo hankalin Shugaban kasa, Bola Tinubu da majalisar kasa kan illar gayyato sojojin Amurka da wasu kasashen Turai na kafa sassanin soja a Nijeriya, bayan da aka fatattake su daga wasu kasashe.
“Matsayar jam’iyyar PRP kan wannan yunkurin dai shi ne, akwai matukar illa ga sha’anin tsaron kasarmu da ‘yancin gashin kai. Domin haka ne muke gargadin gwamnatin Nijeriya ba ma goyon bayan wannan lamari.
“Gayyato wadannan sojoji zuwa kasarmu domin su kafa sassani ba karamin illa ba ce ga harkokin tsaronmu da kuma lafiyar ‘yan ksarmu. Bisa tsarin da aka kafa jam’iyyarmu na samun cikakken ‘yanci, wannan ya saba da ra’ayin kasarmu saboda dalilai da dama.
“Shigowar sojojin zai kara tauye ‘yancinmu wajen shigo da ra’ayoyin ‘yan kasashen ketare a kasarmu ta gado. Sannan za a samu sabon barazana kan harkokin tsaro, domin wadannan sojojin ba su san sha’anin tsaron Nijeriya ba wanda haka ka iya janyo hatsarin ta’addanci da sauran rikice-rikice.
“Dole ne gwamnatin Nijeriya ta yi la’akari da illar da wannan lamari zai yi wa tattalin arziki idan hharr sojojin kasashen waje suka kafa sassaninsu a Nijeriya. Za a samu tsadar masaukin sojojin da kulawa da ababen more rayuwarsu. Bugu da kari, akwai babban illa wajenn kulawa da sojojin kasashen ketare.”
Sai dai kuma, Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris Malagi, ya musanta cewa Nijeriya na shirin amincewa a kafa sansanonin sojin na kasashen waje a kasarta, yana mai cewar masu yamadidi ne kawai suka kitsa maganar kuma suke ta yadawa.
“Ina mai tabbatar wa da ‘yan kasa cewa babu wannan shirin. Akwai kasashen da muke kawance da su don yaki da matsalar tsaronmu, wannan muna ci gaba da yi, amma ba wai batun kafa sansanonin sojojinsu. Jita-jita ce kawai!”.