A kashi na biyu na tattaunawa da MARYAM ABDUL’AZIZ wacce aka fi sani da MAI KOSAI ta bayyana wasu nasarori da kalubalen da suka ci mata tuwo a kwarya a kan harkar rubuta kamar yadda za ku ji daga hirarsu da PRINCESS FATIMA ZARAH MAZADU kamar haka:
Kin rubuta labari sun kai guda nawa?
To gaskiya labaraina suna da yawa, don a kwai wadanda a littafi ne na rubuta su, sun kai guda biyar, sai kuma lokacin dana fara rike babbar waya na fara rubutu a online, to suma na online din a kwai cikakku da wadanda ba cikakku ba, ma’ana a kwai wadanda na fara ban kai ga kammala rubutawa ba, idan zan hade su duka har wadancan na bayan to sun kai 15 a haka ma ban da gajerun labarai dana rubuta.
A cikin labarun da ki ka rubuta, wanne ki ka fi so?
Gaskiya na fi kaunar ‘Biyayya’ saboda na gina littafin ne kan yadda jaruman suka jajirce wajen yi wa iyayensu biyayya a kan abin da ba rayukansu ke so ba, wanda daga karshe suka ga ribar hakan, kuma suka ga ribar hakuri da juriyar abin da suka yi.
Wane labari ne ya fi baki wahala wajen rubutawa?
Labarin ‘Hafsatul-Kiram’ Saboda na sha bincike sosai a kansa, kuma har yanzu ban ma kammala shi ba, don bana jin ko damba na daura a kansa.
Cikin labarun da kika rubuta ko a kwai wanda ki ka buga ciki?
Eh! a kwai wanda na buga, kuma ina saka ran sake buga wasu in sha Allah.
Wane irin nasarori ki ka samu hame da rubutu?
Alhamdu lillah! Na samu nasarori da dama a harkar rubutu, ba abin da zan ce da Allah Madaukakin Sarki sai godiya, domin wannan wata babbar ni’ima ce ya ba ni da ba kowa ya ke bawa ba.
Ko a kwai wani kalubale da kika fuskanta game da rubutu?
Eh! Na fuskanci kalubale musamman a lokacin dana fara rubutun online, duk da dai wacce ta yi min jagora ba ta cuce ni ba, ba ta kuma rage ni da komai ba, don tsakanina da ita har yau har gobe sai godiya da fatan alkhairi. Sai dai shiga ta wata kungiya ya sa na ji na karaya har ina jin kawai gara na hakura na ajjiye harkar rubutu kwata-kwata, saboda an yi min abu ma fi soyuwar ciwon da zuciya da kwakwalwa ba za su kasa mancewa ba. Bangaren masu karatu tsakanina da su sai godiya, don wasu ma baka san su ba haka za su kiraka ko su yi maka magana su ce suna son littafinka. Duk da na taba fuskantar wani kalubale ta bangarensu wanda abun ya ba ni mamaki sosai. Na yi wani littafin kudi ne, sai wata ta biyo ni ‘pribate’ tana tambayata, “Wai ke me ya sa ba kya saka ‘romantic’ a littafinki, da sai ya fi ba da citta? Ina son siyan wannan amma na ga alama kamar babu rakashewa a ciki.”
Abun ya ba ni dariya ya ba ni mamaki, wato idan babu batsa ba za ta siya ba ke nan? To ire-irensu ina samu da dama, da kuma makamanta haka.
Wane abu ne ya taba faruwa da ke na farin ciki ko akasin hakan wanda ba za ki manta da shi ba game da rubutu?
Ba a rasa ba, amma ni idan ma an so a bata min rai kaucewa nake yi, saboda idan ka ce al’amarin mutane za ka yi ta sakawa a gaba to zuciyarka ce za ta haye ta suntuma ta fashe kamar wata bom. Ana yabawa sosai, kuma iyayena sune na farkon da suke yabawa bana damuwa da sauran jama’a idan ba su yaba ba, amma duk da haka ana yabawa daidai gwargwado.
Me ya fi saka ki farin ciki game da rubutu?
Idan ina rubutu na kan tuna baya, lokacin da nake rubutu a boye kamar wacce ta yi abin rashin arziki take tsoron a kamata, to idan ina rubutu na kan tuna sai na ji na dara na shiga kogin walwala.
Ya ki ka dauki rubutu a wajenki?
Gaskiya rubutu a wajena wani babban al’amari ne, wanda ina ganinsa da matukar muhimmanci sosai fiye da kima.
Bayan rubutu kina yin sana’a?
Eh! ina taba harkokin kasuwanci.
Ya kike iya hada rubutu da kuma kasuwanci?
To ina ware lokutan rubutu duk da wani lokacin kwatsam zan ji ‘idea’ ta fado min, daman a kwai biro da takarda kusa da ni, zan maza na rubuta, ko na shigar a wayata. Amma dai duk ina iya hada su waje guda tunda kasuwanci ne kake na online ba shago za ka fita ko kasuwa ba.
Kamar da wane lokacin kika fi jin dadin yin rubutu?
Na fi jin dadin yin rubutu da daddare, kowa ya yi bacci koda Asuba.
Me za ki ce da makaranta littafinki?
Babu abin da zan ce da su sai fatan alkhairi.
Ko kina da wadanda za ki gaisar?
Na farko iyayena, da kannena, na biyu maigidana, na uku Malamaina, na hudu Marubuta gabadayansu kaf! ban ware ko guda ba, na biyar ‘Yan’uwa da abokan arziki.