A jiya ne aka kaddamar da makon yayata ruhin tsimin makamashi a birnin Beijing na shekarar 2024, inda an ce, za a gaggauta matakan amfani da motoci masu aiki da wutar lantarki da aka samar ta amfani da makamashi mai tsabta, da fidda sabon tsarin samar da wutar lantarki ta amfani da makamashi mai tsabta, ta yadda za a habaka boyayen karfi tsakanin bukatun jama’a da makamashin da ake samarwa. Ban da wannan kuma, hakan zai ingiza jama’a su rika amfani da wutar lantarkin da ake samarwa ta amfani da makamashi mai tsabta.
Wannan mataki zai ingiza raya birnin Beijing ba tare da bata muhalli ba, da ingiza muhimmiyar manufar cimma burin kaiwa ga kololuwar yawan hayaki mai dumama yanayi da ake fitarwa, da kuma kokarin samun daidaito tsakanin yawan hayakin da za ta fitar, da yawan abubuwan da za su shawo kan hayakin.
A shekarun baya bayan nan, Beijing ta kara ingiza amfani da wutar lantarkin da aka samar ta amfani da makamashi mai tsabta, da gudanar da sassan gwaji, da cinikin wutar lantarkin yadda ya kamata, matakin da ya habaka kasuwar wannan bangare. Ya zuwa yanzu, yawan wutar lantarki ta amfani da makamashi mai tsabta da aka yi ciniki a bana, ya ninka sau 2.4 bisa na bara. (Amina Xu)