Kungiyar kwadago, a ranar Laraba, ta yi fatali da ta yin da gwamnatin tarayya ta yi mata na biyan mafi karancin albashi ga ma’aikatan Nijeriya akan Naira N48,000.
Kungiyar ta zargi gwamnati da kungiyar kamfanoni masu zaman kansu da ta yin “wulakanci” da abin da suka bayyana a matsayin “tayin ban dariya”.
- Hajjin 2024: Ranar 10 Ga Watan Yuni Za A Kammala Jigilar Maniyyata – NAHCON
- Hukumar NSCDC Ta Kama Wasu Mutane 9 Da Ake Zargi Da Aikata Fashi A Kano
Daily trust ta ruwaito cewa, gwamnati ta yi tayin Naira 48,000, yayin da kungiyar kamfanoni masu zaman kansu su ka amince da Naira N54,000.
A yayin da kungiyar ‘yan kwadago ke nuna takaicinta da tayin a wani taron manema labarai a hedikwatar kungiyar a Abuja, shugabannin kungiyar kwadagon sun ce, gwamnati ba ta bayar da wani bayani ba kan tayinta na biyan Naira N48,000 a matsayin mafi karancin albashi.