Sashin kula da jinyar gaggawa a Nijeriya na fuskantar tulin manyan matsaloli sakamakon rashin wadataccen wuraren gudanar da aiki da karancin motocin daukan marasa lafiya na gaggawa, da kuma asarar kudaden jinyar gaggawa na biliyan 26.3 da hakan ke tasiri wajen rage kaifin kokari da suke yi.
Binciken LEADERSHIP ya gano cewa kudaden naira biliyan 26.3 na jinyar gaggawa baya shiga kai tsaye ga asibitocin da ke kula da jinyar gaggawa ke amfani da su ga marasa lafiya a lokacin da bukatar hakan ta taso.
- Sin: Karbuwar Hajojin Sin Masu Nasaba Da Sabbin Makamashi Ba Shi Da Nasaba Da Samar Da Tallafi
- Za A Bude Shafin Karbar Bashin Dalibai A Ranar 24 Ga Mayu
Kudaden wanda kwatankwacin kaso biyar na asusun tallafin kiwon lafiya (BHCPF) ya bace ne cikin shekaru bayan da dokar kiwon lafiya da aka yi domin amfani da kudaden wajen gudanar da ayyuka na musamman a lokacin da ake halin bukatar jinyar gaggawa.
A tsakanin shekarar 2020 da 2024, an amince da naira biliyan 526.9 wa shirin tallafin kiwon lafiya BHCPF, kaso biyar cikin dari sun haura naira biliyan 26.3.
Wannan kuma na zuwa ne a daidai lokacin da kudaden da ake kashewa wajen kula da marasa lafiya da suka tsinci kansu a bukatar agajin gaggawa ya lakume sama da naira biliyan 200 a cikin shekaru goma da suka wuce, duk da cewa likitoci masu zaman kansu a Nijeriya sun yi kira ga gwamnati da ta fitar da kaso 2.5 cikin dari na kudaden tallafin kiwon lafiya (BHCPF) domin jinyar gaggawa.
Kula da agajin gaggawa, babu shakka na da muhimman rawa a tsarin kiwon lafiya a Nijeriya. A cewar wani binciken da aka gudanar a 2019, kaso uku cikin hudu na ‘yan Nijeriya a kalla sau daya a rayuwarsu sun taba fuskantar jinyar gaggawa a cikin shekaru biyar da suka gabata, yayin da kusan kaso daya cikin hudu na ‘yan Nijeriya sun taba fuskantan jinyar gaggawa sama da sau hudu a rayuwarsu.
Yanayin lafiya na yau da kullum da hatsarin ababen hawa sun taimaka sosai wajen janyo jinyar gaggawa da daman gaske a kasar nan. A misali, adadin yawaitar hatsarin ababen hawa a zangon karshe na shekarar 2022, ya kai 3,617, lamarin da ke nuni da cewa an samu kari da kaso 6.01 daga na zangon da ya gabaci wannan da aka samu yawan hatsari 3,412, da kuma karin kaso 6.16 daga adadi 3,407 da aka samu a zangon karshe na 2021, kamar yadda hukumar kiddiga ta Nijeriya (NBS) ta sanar.
Rahoton NBS ya cewa an samu aukuwar hatsarin ababen hawa sama da 11,800 a Nijeriya a tsakanin watan Oktoba da Disamban 2021; inda a kalla mutum 10,200 suka raunata, yayin da kuma 1,700 suka mutu a wannan tsakanin.
Wani binciken ilimi mai taken ‘yawaitar mace-mace sakamakon hatsarin ababen hawa, sashin jinyar gaggawa a asibitocin birane da ke Nijeriya’ ya yi nuni da cewa mafi yawan mace-macen da aka samu sakamakon aukuwar hatsarin ababen hawa na wakana ne cikin awanni shida gabanin a kawo majinyata daga inda aka samu aukuwar hatsari zuwa cibiyoyin kula da agajin gaggawa da suke cikin asibitocin biranen Nijeriya.
Domin dakile wannan mace-macen da shan wahalar jinyar, tsohon shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani shirin tallafin kiwon lafiya ta BHCPF kuma ya shigar da shi cikin kasafin da ya tura wa majalisar dokoki na kasa a karin farko a 2018, tun bayan kafa dokar kiwon lafiya na kasa (NHAct) a shekarar 2014.
A bisa yadda yake a dokar kiwon lafiya ta kasa na 2014, tallafin kiwon lafiya BHCPF na samun kudi ne daga kason shekara-shekara daga gwamnatin tarayya wanda bai yi kasa da kaso daya na harajin (CRF) ba; da ake samu daga kungiyoyin tallafin kasashen waje da kudaden da ake samu daga sauran bangarori ciki har da kamfanoni masu zaman kansu.
Kuma dokar ya fayyace yadda za a sake kudaden da suka shafi shirin BHCPF da rabe-rabensu ya kasu zuwa gida uku, daga cikin hanyoyin da ake sake kudaden akwai ta shirin taimakeniyar kiwon lafiya na kasa (NHIS) da kuma ‘Basic Minimum Package Health Scheme’ (BMPHS) da manya da kananan asibitoci ke cin gajiya.
Hudu zuwa biyar na kason kudin an tsara cewa zai fita ne ta hannun hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko ta kasa (NPHCDA) da shi kuma kai tsaye zai kasafta zuwa kananan asibitocin kiwon lafiya (PHCs) da za su samu damar sayen magungunan da kayan jinya, rigakafi, kayan kula da asibitocinsu, da kayan aiki hadi da na zirga-zirga; da sashin kula da ma’aikata. Kuma dole ne kaso 2.5 na wannan kudin a fitar da shi ta hannun kwamitin da majalisar kiwon lafiya (NCH) ta kafa da niyyar kula da jinyar da suka shafi agajin gaggawa da kuma wani kaso 2.5 da zai tafiya kai tsaye zuwa cibiyar dakile yaduwar cutuka ta kasa (NCDC).
A halin yanzu tallafin da ya shiga cikin lalitar shirin BHCPF sun kunshi biliyan naira 88,993,570,146.91 wanda naira biliyan 59,203,966,455.42 aka raba ga jihohi zuwa watan Yuni na 2022, kamar yadda binciken jaridar LEADERSHIP ya gano.
Shugaban kungiyar likitoci masu zaman kansu (ANPMP), Dakta Kayode Adesola ya shaida wa LEADERSHIP cewa sashi na 20(1) na dokar kiwon lafiya ta kasa NHAct (2014) ya tanadar da cewa, “Asibiti, jami’in kiwon lafiya ko wata cibiyar jinya wajibi ne a garesu ka da su ki bayar da jinya ga kowani mutumin da yake halin jinya na gaggawa.”
“Tun daga 2014, mu likitoci masu zaman kanmu muna jinyar gaggawa, kamar yadda yake cikin kundin dokar, ba tare da an biya mu sisi ba. A bisa lissafinmu, muna bin kudin ayyukan kiwon lafiya na gaggawa a cibiyoyin jinya sama da 11,000 da suke Nijeriya fiye da Naira biliyan 200 daga shekarar 2012 zuwa yanzu,” Adesola ya tabbatar.
Da yake magana kan kokarinsu na ganin sun dawo da kudadensu, shugaban ya ce, “Muna sane da cewa kaso 2.5 na kudaden tallafin kiwon lafiya na shirin BHCPF an ware ne na musamman domin jinyar kesa-kesan da suke na gaggawa. Mun je majalisar dokoki na kasa muna rokon su da kaddamar da binciken ta ina wadannan kudaden suke sulalewa. Asibitoci masu zaman kansu a Nijeriya suna samun kesa-kesan jinyar gaggawa sosai ba tare da ana biyansu sisin kwabo ba. Kuma, wani mutum zai iya tsintar kansa a halin jinya na gagagwa.”
Adesola y ace idan gwamnati ta ki biyan kudaden, za su ci gaba da kula da jinyar a matsayin na jin kan jama’a ba za su taba dainawa, sai dai ya ce kuma hakan zai zama abun kunya a ce gwamnati ta sanya hukunci ga wani likitan da ya ki jinyar wani da ke halin gaggawa a bisa doka sashi na 20(1) na dokar kiwon lafiya ba tare da ana biyansu ko sisi ba, duk da an ware kudi don haka.
Kan hakan ne ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su matsa wa gwamnati ta sake musu wannan kudaden, “Muna kira ga majalisar dattawa da ta taimaka ta duba wannan batun ta yi bincike kan inda kudaden suke,” Adesola ya tabbatar.
Mataimakin shugaban kwamitin kiwon lafiya na majalisar dattawa, Sanata Samaila Kaila, ya tabbatar da cewa tsarin kiwon lafiya a Nijeriya ba ya tafiya kan irin wannan layin, inda ya nuna cewar majalisar za ta binciki lamarin tare da yin abubuwan da suka dace.
Sai dai kuma, CMD na asibitin koyarwa ta jami’ar Uyo, Emem Bassey, ya tabbatar da cewa kaso 2.5 na jinyar kesa-kesan gaggawa na can a lalitar ma’aikatar kiwon lafiya.