Kwaminshinan Masana’antu da cinikayya da saka hannun jari na Jihar Nasarawa, Batista Abubakar Imam Zanwa ya bayyana irin alherin da al’umman garin Lafiya suka samu na hadin kai a iya shekarun da Sarki Sidi Bage ya yi kan karagar mulkin masarautan Lafiya.
Ya ce Sarki Sidi Muhammad Bage ya gaji Sarki Isa Mustapha wajen yada alheri cikin kasa. Ya ce Sarki Isa Mustapha ya yi shekaru sama da 40 kan karaga, ya kuma ya yi kokari wajen samun ci gaban Jihar Nasarawa.
- Za A Bude Shafin Karbar Bashin Dalibai A Ranar 24 Ga Mayu
- Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Hanyar Tafiyarsu Ta Kai Hari Ga Al’ummar Jihar Kaduna
A cewar kwamishinan, Sarki Sidi da yake kwararene a bangaren shari’a, wanda yayi alkalanci tun daga karamar kotu har zuwa kotun koli ta kasa, ya yi amfani da gogewa wajen kara saita Jihar Nasarawa bisa turbar ci gaba kamar yadda Sarki Isa Mustapha Agwai ya yi.
Ya ce Sarki Sidi ya yi amfani da tsarin shari’a a matsayinsa na Shugaban Majalisan Sarakunan Jihar Nasarawa ya jagoranci Sarakunan jihar zuwa turbar hadin kai da rungumar kowani dan jihar Nasarawa da bai wa gwamnati goyon baya, saboda tabbatar da zaman lafiya.
Ya ce matujar sarakuna za su tsawatar da al’umma, su kyamaci cin zarafin addinan da kawar da bambamcin kabila, to za a samu zaman lafiya cikin Jihar Nasarawa.
Kwamishinan ya kara da cewa cikin shekaru biyar da Sarki Sidi ya yi kan kujerar mulki ya samar da abubuwan alheri da matasa za su amfana.