• English
  • Business News
Sunday, September 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Ganawar Manyan Jam’iyyun Adawa Ta Kara Wa Yunkurin Maja Kaimi

by Yusuf Shuaibu
1 year ago
in Tambarin Dimokuradiyya
0
2027: Ganawar Manyan Jam’iyyun Adawa Ta Kara Wa Yunkurin Maja Kaimi
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Ziyarar da dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 karkashin jam’iyyar LP, Peter Obi ya kai wa manyan kusoshin ‘yan siyasa na kasa ciki har da dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar ta haifar da zazzafar muhawara tare da bude babin yunkurin da ‘yan adawa ke yi na kwace mulki a hannun APC a zaben 2027.

Atiku ya wallafa hotunan ganawar a shafinsa na Tuwita tare da bayyana cewa abun alfahari ne a gare shi a yau da ya karbi bakoncin Peter Obi.

  • Zanga-zangar Karin Kudin Wuta: Gwamnati Ta Shelanta Matakin Da Za Ta Dauka
  • Ziyarar Xi Jinping A Turai Ta Fitar Da Muryar Kiyaye Zaman Lafiya Da Yin Hadin Gwiwa

Daya daga cikin mataimakan Atiku wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana cewa ganawar ta kasance ta sirri ce, amma har yau Atiku yana nan kan bakansa na ganin jam’iyyun adawa sun yi maja domin kwace mulki a hannun APC.

Haka shi ma mai magana da yawun dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Yunusa Tanko ya ce, tabbas wannan ganawa ce ta sirri kuma babu wani abu idan mutum ya ziyarci tsohon abokinsa.

 Ya kara da cewa a duk lokacin da irin wadannan mutane suka tattauna batutuwa daban-daban, to abin da ake fata a karshen tattaunawar ya zama ya amfani ‘yan Nijeriya baki daya.

Labarai Masu Nasaba

Rudani Ya Kunno Kai Yayin Da INEC Ta Ki Amincewa Da Shugabancin ADC

‘Yan Nijeriya Suna Shan Wahala A Lokacin Da Gwamnatin Tinubu Ta Fi Damuwa Da Aljihunta – Sule Lamido

Kafin ya ziyarci Atiku, Obi ya yi ganawar sirri da tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido a gidansa da ke Abuja. Mataimaki na musamman ga Lamido, Mansur Ahmed ya tabbatar da wannan ziyarar, inda ya ce shugabannin guda biyu sun gudanr da wata ganawa ta sirri.

Sannan kuma, a wata sanarwa da Tanko ya fitar ya ce Peter Obi ya kuma ziyarci tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.

“A dukkanin wadannan ziyarce-ziyarce an tattauna batutuwan da suka shafi kasa ta yadda za a rage wa ‘yan Nijeriya wahalhalun da suke ciki ba tare da la’akari da matsayinsu ko kuma wurin da suke zaune ba. Musamman ma an yi tsokaci kan matsin rayuwa da al’ummar Nijeriya ke ciki.

“Wani abu mai muhimmanci da aka tattauna a wadannan ziyarce-ziyarce shi ne, halin da ake ciki a yankin arewacin Nijeriya,” in ji sanarwar.

Peter Obi ya kasance mataimakin dan takarar shugaban kasa na Atiku a zaben 2019, inda ya raba gari da tsohon mataimakin shugaban kasan daga bisani, wanda ya zama dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, sakamakon kiraye-kirayen da ake yi masa ya bar PDP ya koma wata jam’iyya domin ya samu damar tsayawa takara.

Yayin da Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya zama wanda ya yi nasara a zaben 2023 da kuri’u 8,794,726, masana harkokin siyasa sun yi hasashen cewa Atiku da Obi za su sake neman tikitin takara da su bai wa jam’iyya mai mulki ciwon kai.

Atiku ya samu kuri’u 6,984,520, yayin da Obi ya samu kuri’a 6,101,533. Dukkaninsu biyun sun samu kuri’u 11,262,978 a zaben 2019, yayin da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya samu kuri’u 15,191,847.

Ziyarar da Obi ya kai wa Atiku a ranar Litinin, ta zo ce kwana guda bayan da mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe, a wata tattaunawa ya nanata cewa, Atiku bai tilasta wa Obi barin PDP ba, amma ya zargi ministan Abuja, Nyeson Wike da zama dalilin barin Obi jam’iyyar PDP.

“Atiku Abubakar bai tilasta wa Obi ficewa daga PDP ba. Atiku yana matukar kulawa da dangantakar da ke tsakaninsa da Obi,” in ji Ibe.

Idan za a iya tunawa dai, tun bayan kamala zaben 2023, Atiku yana kan gaba wajen bukatar jam’iyyun adawa su kafa kawancen kwace mulki a hannun jam’iyyar APC a zaben 2027.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: AdawaJam'iyyaPDP
ShareTweetSendShare
Previous Post

Yadda Ƙungiyar Matasan Arewa Kan Harkokin Tsaro Ta Shirya Tattaunawa Kan Batun ‘Yansandan Jihohi

Next Post

Wutar Lantarki Ta Yi Ajalin Wani Mutum A Bayelsa

Related

Fursunoni Ba Za Su Samu Damar Kada Kuri’a Ba A Zaben 2023 – INEC
Tambarin Dimokuradiyya

Rudani Ya Kunno Kai Yayin Da INEC Ta Ki Amincewa Da Shugabancin ADC

1 week ago
‘Yan Nijeriya Suna Shan Wahala A Lokacin Da Gwamnatin Tinubu Ta Fi Damuwa Da Aljihunta – Sule Lamido
Tambarin Dimokuradiyya

‘Yan Nijeriya Suna Shan Wahala A Lokacin Da Gwamnatin Tinubu Ta Fi Damuwa Da Aljihunta – Sule Lamido

1 week ago
Daraktoci Da Jami’an FCT 7 Na Fuskantar Tuhume-tuhume Kan Badakar Fili
Tambarin Dimokuradiyya

2027: Idan Kana Son Tarwatsa PDP, To Ka Dawo Da Peter Obi – Wike

1 week ago
ADC Ta Bukaci Tinubu Ya Kafa Dokar Ta Baci A Katsina Da Zamfara Kan Rashin Tsaro
Tambarin Dimokuradiyya

ADC Ta Bukaci Tinubu Ya Kafa Dokar Ta Baci A Katsina Da Zamfara Kan Rashin Tsaro

2 weeks ago
katin zabe
Tambarin Dimokuradiyya

INEC Ta Bayyana Damuwarta Kan Katunan Zabe 360,000 Da Ba A Karba Ba A Kano

2 weeks ago
Jam’iyyar PDP Ta Janye Daga Shiga Zaɓen Ƙananan Hukumomi A Kebbi
Tambarin Dimokuradiyya

Shugabannin PDP Sun Shiga Dimuwa Yayin Da APC Ke Zawarcin Wasu Gwamnoninsu

2 weeks ago
Next Post
Wutar Lantarki Ta Yi Ajalin Wani Mutum A Bayelsa

Wutar Lantarki Ta Yi Ajalin Wani Mutum A Bayelsa

LABARAI MASU NASABA

Matashi Ya Rasa Ransa A Yunƙurin Satar Kyabul Ɗin Taransifoma A Maiduguri

Matashi Ya Rasa Ransa A Yunƙurin Satar Kyabul Ɗin Taransifoma A Maiduguri

September 14, 2025
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

An Kama Wani Sojan Gona Ɗauke Da Bindiga A Katsina

September 14, 2025
Rashin Tsaro Ya Sa Ƴan Gudun Hijira Mamaye Makarantun Benuwe Da Neja Da Katsina

NPA Ta Fara Aiki Da Sabon Tsarin ETO A Tashar Apapa

September 14, 2025
Sojojin Nijeriya Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 139, Sun Cafke 132 A Cikin Sati 2 —Hedikwatar Tsaro

Sojoji Sun Ceto Mutane 30 Da Aka Yi Garkuwa Da Su, Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Da Dama

September 14, 2025
Ɗalibai 750 Sun Amfana Da Bashin Karatu Na Naira Milyan 32.14 A Jihar Gombe

Ɗalibai 750 Sun Amfana Da Bashin Karatu Na Naira Milyan 32.14 A Jihar Gombe

September 14, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas

‘Yansanda Sun Ceto Yara 5 Da Aka Sace A Adamawa

September 14, 2025
Rashin Tsaro Ya Sa Ƴan Gudun Hijira Mamaye Makarantun Benuwe Da Neja Da Katsina

Dawowa Hutu Ya Tayar Da Hankalin Iyaye Saboda Ƙarin Kuɗin Makaranta

September 14, 2025
Likitoci

NARD Ta Janye Yajin Aikin Gargaɗi Da Ta Fara

September 14, 2025
APC Na Ƙoƙarin Tarwatsa Mu Ne Saboda Kar Mu Ƙwaci Mulki A 2027 – ADC

APC Na Ƙoƙarin Tarwatsa Mu Ne Saboda Kar Mu Ƙwaci Mulki A 2027 – ADC

September 14, 2025
An Cafke Bature Ɗan Shekara 37 Kan Mutuwar Ɗan Nijeriya Mazaunin Birtaniya

An Cafke Bature Ɗan Shekara 37 Kan Mutuwar Ɗan Nijeriya Mazaunin Birtaniya

September 14, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.