Ziyarar da dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 karkashin jam’iyyar LP, Peter Obi ya kai wa manyan kusoshin ‘yan siyasa na kasa ciki har da dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar ta haifar da zazzafar muhawara tare da bude babin yunkurin da ‘yan adawa ke yi na kwace mulki a hannun APC a zaben 2027.
Atiku ya wallafa hotunan ganawar a shafinsa na Tuwita tare da bayyana cewa abun alfahari ne a gare shi a yau da ya karbi bakoncin Peter Obi.
- Zanga-zangar Karin Kudin Wuta: Gwamnati Ta Shelanta Matakin Da Za Ta Dauka
- Ziyarar Xi Jinping A Turai Ta Fitar Da Muryar Kiyaye Zaman Lafiya Da Yin Hadin Gwiwa
Daya daga cikin mataimakan Atiku wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana cewa ganawar ta kasance ta sirri ce, amma har yau Atiku yana nan kan bakansa na ganin jam’iyyun adawa sun yi maja domin kwace mulki a hannun APC.
Haka shi ma mai magana da yawun dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Yunusa Tanko ya ce, tabbas wannan ganawa ce ta sirri kuma babu wani abu idan mutum ya ziyarci tsohon abokinsa.
Ya kara da cewa a duk lokacin da irin wadannan mutane suka tattauna batutuwa daban-daban, to abin da ake fata a karshen tattaunawar ya zama ya amfani ‘yan Nijeriya baki daya.
Kafin ya ziyarci Atiku, Obi ya yi ganawar sirri da tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido a gidansa da ke Abuja. Mataimaki na musamman ga Lamido, Mansur Ahmed ya tabbatar da wannan ziyarar, inda ya ce shugabannin guda biyu sun gudanr da wata ganawa ta sirri.
Sannan kuma, a wata sanarwa da Tanko ya fitar ya ce Peter Obi ya kuma ziyarci tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.
“A dukkanin wadannan ziyarce-ziyarce an tattauna batutuwan da suka shafi kasa ta yadda za a rage wa ‘yan Nijeriya wahalhalun da suke ciki ba tare da la’akari da matsayinsu ko kuma wurin da suke zaune ba. Musamman ma an yi tsokaci kan matsin rayuwa da al’ummar Nijeriya ke ciki.
“Wani abu mai muhimmanci da aka tattauna a wadannan ziyarce-ziyarce shi ne, halin da ake ciki a yankin arewacin Nijeriya,” in ji sanarwar.
Peter Obi ya kasance mataimakin dan takarar shugaban kasa na Atiku a zaben 2019, inda ya raba gari da tsohon mataimakin shugaban kasan daga bisani, wanda ya zama dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, sakamakon kiraye-kirayen da ake yi masa ya bar PDP ya koma wata jam’iyya domin ya samu damar tsayawa takara.
Yayin da Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya zama wanda ya yi nasara a zaben 2023 da kuri’u 8,794,726, masana harkokin siyasa sun yi hasashen cewa Atiku da Obi za su sake neman tikitin takara da su bai wa jam’iyya mai mulki ciwon kai.
Atiku ya samu kuri’u 6,984,520, yayin da Obi ya samu kuri’a 6,101,533. Dukkaninsu biyun sun samu kuri’u 11,262,978 a zaben 2019, yayin da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya samu kuri’u 15,191,847.
Ziyarar da Obi ya kai wa Atiku a ranar Litinin, ta zo ce kwana guda bayan da mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe, a wata tattaunawa ya nanata cewa, Atiku bai tilasta wa Obi barin PDP ba, amma ya zargi ministan Abuja, Nyeson Wike da zama dalilin barin Obi jam’iyyar PDP.
“Atiku Abubakar bai tilasta wa Obi ficewa daga PDP ba. Atiku yana matukar kulawa da dangantakar da ke tsakaninsa da Obi,” in ji Ibe.
Idan za a iya tunawa dai, tun bayan kamala zaben 2023, Atiku yana kan gaba wajen bukatar jam’iyyun adawa su kafa kawancen kwace mulki a hannun jam’iyyar APC a zaben 2027.