Assalamu alaikum masu karatu barkaN mu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
A yau shafin na mu zai kawo muku yadda ake Kosan Dankali da Nama iri biyu, na farko mai laushi, na biyu kuma mara laushi.
Mai Laushi
Abubuwan da za ki tanada:
Dankali, Nama, Kwai, Attarugu, Albasa, Magi, Gishiri, Mai, Fulawa Ko Garin Busashen Buredi.
Yadda za ki hada:
Da farko ki wanke nama ki zuba a tukunya sai ki zuba magi da gishiri ki tafasa sai ki kwashe ki zuba a turmi ki daka tare da albasa da attaruhu idan ya yi laushi sai ki kwashe a kwano ko roba, sannan ki dawo kan dankalin turawa ki tafasa ya yi laushi sai ki murmushe shi ko kuma ki daka shi a turmi sai ki kwashe shi a cikin kwanon da kika kwashe naman da kika daka, sai ki dauko kwai danye ki fasa a kai, ki zuba fulawa ko garin busashen buredi a ciki ki sa gishiri da magi ki juya sosai, sai ki dauko abin suya ki zuba mai ki dora a kan wuta ki dinga diba da cokali kina zubawa a cikin man idan ya yi zafi idan ya soyu za ki ga ya yi kalar kasa-kasa sai ki kwashe. A ci dadi lafiya.
 Mara Laushi
Abubuwan da za ki tanada:
 Dankalin Turawa, Nama, Fulawa, Kwai, Albasa, Attarugu, Gishiri, Magi, Mai
Yadda za ki hada:
Ki jajjaga albasa da attarugu ki kwashe a kwano ko roba sai ki dauki dankali ki tafasa ki zuba a turmi ki daka shi amma kar ya yi laushi sai ki kwashe a cikin kwanon da kika zuba jajjagen attarugu da albasa ki tafasa naman shi ma ki daka a turmi duk ki hada da sauran kayan hadin ki juya, sai ki dinga mulmulawa kina tsomawa a ruwan kwai ki juya shi a cikin fulawa ki jefa a cikin man mai zafi ki soya, shi kenan kin gama. A ci dadi lafiya.