Kamar yadda Mudathir Ishak ya yi tsokaci an kafa birnin Zazzau ne a shekarar 1536, miladiyya,a wani yanki na dausayi, kudu da hamada, maraya ce da ta hada manoma da kuma malamai da masu kasuwanci.Sarkin Farko a wancan lokaci sunansa Gunguma dan Bawo.
Bawo kuwa a Hausance shine Bayajidda na Sarauniyar Daurama. Zariya ita ce kanwa ga Sarauniya Amina shine kuma sunan da ta baiwa babban birnin Zazzau,kusa da dutsen Kufaina,a cikin karni na 16 ne aka sanya wa Zazzau wannan suna.
- Sojoji Sun Aike Da Ƴan Ta’adda 8 Lahira, Sun Daƙile Yunƙurin Sace Wasu Mutane 28
- Takaitaccen Nazari A Kan Bishiyar Kanya
Sarauniya Zariya ta gaji Amina wadda rasu a shekarar 1610 miladiyya a garin Attagara, bayan da ta ci Kano da Katsina da yaki.
Ita ma ta rasu a Yawuri ne, bayan da tayi gajeren mulki. Fadin iyakar inda ta ci da yaki ya kai daga jihar Filato ta yanzu a gabas, zuwa Abuja da kewaye, kamar su Nupe da Nasarawa.
A Arewa kuma har Daura da Katsina ta hadiyo.Ta kuma ta shafe shekaru 30 tana mulki. Mahaifiyarsu ita ce Bakuwa Turunku,ta 22 a jerin sarakunan Zazzau, kafin zuwan fulani. Ita ta kafa garin Turunku, kudu da Zazzau ko Zariya,a kan hanyarta ta zuwa yake-yake da kabilun Nupawa da Gwarawa.Jerin sunayen sarakunan gargajiya da aka yi a Zazzau. Kafin dai fulani su ci Zariya da yaki,a shekarar 1807,an yi sarakuna 60 Hausawa ‘yan asalin garin da yankin, watau sarakunan Habe, wadanda wasunsu sun bi addinan gargajiya, yayin da wasu suka yi addinin musulunci. Sarki Jatau dai a tarihi, wanda yayi mulki ne daga shekarar 1742 zuwa 1802 shi ya fara musulunta ya kuma gina masallaci na farko. Bayan rasuwarsa,sai dansa Makau, ya koma addinin gargajiya, ya kuma rushe masallacin.
Sai dai kuma a shekarar 1804 ce, da Usmanu dan Fodiyo ya fara yin jihadi, Malam Musa, wanda malami ne kuma bafillace,ya je Gobir inda ya karbo tuta daga Shehu,daganan ya hada karfi da Yamusa, wanda shi ma bafillatanin Borno ne, suka kawo wa Makau yaki. Haka ya sa Makau ya tsere zuwa garin Zuba, inda kusa da inda Babban Birnin Tarayya Abuja take a yanzu, a can ne ya rayu da kabilun yankin har dai ya kai ga rasuwa a can.Malam Musa sai suka tabbatar da abin da mahaifinsa ya faro,watau Masallaci da addinin Islama.
Malam Musa shi ne Sarkin Fulani na Farko, amma ya rasu a a shekarar 1821,daga nan sai Yamusa ya amshi mulki, inda yayi mulki har ya zuwa shekarar 1834.Daga nan sai Malam Abdulkarim, wanda shi bakatsinene kuma bafillace, ga shi dalibi ga Malam Musa ya karbi mulki.Kuma daga wadannan gidaje ne har yau, ake samar da sarakunan Zariya.1. Mallam Musa (gidan Mallawa) 1804-1821 2. Yamusa (gidan Barnawa) 1821-1834 3. Abdulkarim (gidan Katsinawa) 1834-1846 .4 Hamadu dan Yamusa 1846 5. Muhamman Sani dan Yamusa 1846-1860 6. Sidi Abdulkadir dan Malam Musa 1860 (ture shi aka yi)7.Abdussalami (sullubawa) 1860-1863 8. Abdullahi dan Hamadu dan Yamusa 1863-1873 (an ture shi) sai a 1876-1881 (aka sake ture shi) 9. Abubakar dan Malam Musa 1873-1876 l0. Sambo dan Abdulkarim ( gidan Katsinawa)1881-1890 (shima tumbuke shi aka yi) 11. Yero dan Abdullahi dan Hamadu 1890-1897 12. Kwasau dan Yero 1897-1902 (tumbuke shi aka yi) Zuwan Turawa 13. Aliyu Dan sidi Abdulkadir 1902-1923(shima an tumbuke shi) 14.Dallatu dan Yero 1923-1924 15. IIbrahim dan Kwasau 1924-1936 16. Malam Ja’afar dan Ishak 1936-1959 17. Alamin dan Usman 1959-1975 18.Shehu Idris 1975 zuwa shekarar 2020, daga shi kuma sai Ahmad Nuhu Bamalli wanda aka nada sarauta ranar 8 ga Oktoba 2020 zuwa yanzu.Turawa sun iso da rundunoni na yaki har biyu, a 1900 domin mulkin mallaka.
Jerin sarakunan Suleja da ake kiran su da Sarkin Zazzau Suleja wadanda asalinsu daga can suke.
- Muhammadu Makau 1807-1825.
- Abubakar Ja (Abuja) 1825-1851.
- Abubakar Kwaka Dogon Sarki 1851-1877.
- Ibrahim Iyalai Dogon Gwari 1877-1902.
- Muhammadu Gani 1902-1917 Ya bar gadon mulki.
- Musa Angulu 1917-1944
An samo wannan Tarihin ne daga encyclopedia ta Hausa