ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tarihin Gambo Sawaba (1)

by Idris Aliyu Daudawa
9 months ago
Sawaba

An haifi Hajiya Hajaratu Gambo Sawaba a shekarar 1933 a birnin Zariya, Jihar Kaduna. Sunan Mahaifinta, Isaac Dakwada, wanda shi ɗan asalin ƙasar Ghana ne, yayin da kuma ita  mahaifiyarta da ake kira da suna Fatima ta fito ne daga cikin kabilar Nupawa. Yarintarta ko nace ƙuruciyarta ta cika da nauyin da ya  fara yi mata yawa tun da wuri, bayan rasuwar mahaifinta tana ƙarama, sannan kuma da mutuwar mahaifiyarta ba da jimawa ba.

Tun tana yarinya, Hajiya Gambo wadda ta saba da yin gwagwarmaya, inda ta nuna ƙarfin hali da kuma nuna shi ’yanci wani abu ne mai daɗi. Ta yi karatu a ne a Makarantar Natiɓe Authority da ke Tudun Wada, Zariya, amma iliminta ya tsaya ne bakin iyakar Firamare  a sanadiyar auren da aka yi mata tun tana kusan ‘yar shekara 13—wannan kuma  a wancan lokacin wani abu da ya zama ruwan dare game duniya a Arewacin Nijeriya. Ko da yake auren da tayi bai daɗe ba, wannan ne ya buɗe mata ido kan buƙatar cewa mata suna da ’yancin  su yi zaɓe kai har ma suna iya zama wakilan al’umma a majalisu, wannan kuma ta ɓangaren harkar siyasa ne.

  • Daga Sawaba Zuwa Asara: Baje Kolin Kasuwancin Siyasa A Kano – Auwalu Anwar
  • Sin Na Maraba Da ’Yan Jaridar Duniya Da Su Halarci Bikin Cika Shekaru 80 Da Cimma Nasarar Yakin Kin Harin Japan Da Na Tafarkin Murdiya 

Rayuwarta ta sirri ta shahara da aure-aure masu yawa inda har sai da  ta yi aure har sau  biyar baki ɗaya inda  kuma mijinta na huɗu, ana kiransa da suna Abubakar. Duk da cewa aurarrakain da ta yi sun kasance da manyan matsaloli na ƙalubale, ita ce ta ke ɗaukar gabarar ɗawainiyarsu data tafiyar da gida, haka ta haɗa abin ga kulawa da gida, ta waje ɗaya ga kuma lamarin  gwagwarmayar siyasa  wadda a wancan lokacin tana da matuƙar haɗari.

ADVERTISEMENT

Gambo Sawaba ta shiga siyasa tun tana  matashiya, inda ta  zama ‘yar jam’iyyar Northern Elements Progressiɓe Union wato (NEPU), jam’iyyar marigayi Malam Aminu Kano, wadda daga baya kuma aka sauaya mata suna zuwa PRP People’s Redemption Party  babbar  jam’iyyar adawa ce d take da mai tsattsauran ra’ayi, da take  ƙalubalantar waɗanda suke da mulki a hannunsu bama a Arewa kaɗai ba sai da ta mulki Nijeriya  Jam’iyyar NPC Jam’iyyar su Abubakar Tabawa Balewa Ahmadu Bello Sardauna Sakkwato da dai sauran  manyan ƴan siyasa. Ta kasance ɗaya daga cikin muryoyin mata da suka fi ƙarfi  a  cikin jam’iyyar, tana yaɗa manufofin bai wa mata ’yancin yin zaɓe, shiga siyasa, ilimi da kuma kariya daga wasu  munanan al’adun da basu zama dole sai an yi su ba.

Gwagwarmayar  da take yi ne bayan data  fito  a filihakan yasa ta  samu girmamawar manyan Shugabanni na ƙasa, ciki har da jagoran siyasar Kudu maso gabashin Nijeriya Dakta Nnamdi Azikiwe, wanda ake cewa shi ne ya  kira da  sunan mai laƙabin “Sawaba”—abinda yake nufin ’yanci a kalmar Hausa.

LABARAI MASU NASABA

Tarihin Shugaban Makaranta Na Farko A Arewa Hedimasta (2)

Cin Amana Uku Da Suka Sauya Tarihi A Duniya

Sawaba
Idris Aliyu Daudawa
+ postsBio
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tarihin Rayuwar Galadiman Kano Alhaji Tijjani Hashim (2)
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kyamar Baƙi: An Sake Kwaso Ƴan Nijeriya 83 Daga Afirka Ta Kudu
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kamfanin Simintin Dangote Ya Tallafa Wa Manoma 60 Da Kayan Aiki A Edo
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tsohon Shugaban Ƙasa Jonathan Ya Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Ƙasa 18 A Jihar Bauchi

MASU ALAKA

Laifukan Intanet: Kotun Abuja Ta Karɓi Rahoton DSS, Ta Ba Da Belin Wani Ɗan Gwagwarmaya
Tarihi

Tarihin Shugaban Makaranta Na Farko A Arewa Hedimasta (2)

May 30, 2026
Cin Amana Uku Da Suka Sauya Tarihi A Duniya
Tarihi

Cin Amana Uku Da Suka Sauya Tarihi A Duniya

February 22, 2026
Tarihin Sarkin Zazzau Ja’afaru Dan Isiyaku 1936-1959
Tarihi

Tarihin Sarkin Zazzau Ja’afaru Dan Isiyaku 1936-1959. (2)

January 11, 2026
Next Post
Matsalar Rashin Yarda Tsakanin Ma’aurata

Matsalar Rashin Yarda Tsakanin Ma’aurata

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.