Rundunar ƴansandan Nijeriya reshen jihar Kano ta sha alwashin yin aiki da umurnin wata babbar kotun tarayya da ta haramta wa gwamnatin jihar Kano aiwatar da dokar da aka soke da ta shafi masarautar Kano.
Wannan umarnin kotun, wanda mai shari’a Mohammed Liman ya bayar, ya haramtawa Gwamna Abba Yusuf mayar da Sarki Muhammadu Sanusi II kan mukaminsa, tare da dakatar da soke masarautun Bichi da Gaya da Ƙaraye da kuma Rano.
- Gwamnan Kano Ya Bada Umarnin Kamo Tsohon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero
- Yadda Sarki Sunusi Lamido Ya Yi Bikin Shiga Fadar Kano Tsakar Dare
Duk da umarnin da kotu ta bayar, Sarki Sanusi ya jagoranci sallar Juma’a a gidan gwamnati inda daga bisani ya shiga fadar da ƙarfe 1:30am na dare Asabar. Sai dai jim kaɗan da shigowar Sarki Sanusi, tsohon Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya koma jihar inda ya zauna a wata ƙaramar fada da ke Nassarawa. Gwamna Yusuf ya bayar da umarnin a kamo Sarki Aminu Bayero, inda ya zarge shi da yunƙurin tayar da zaune tsaye.
A yayin ganawa da manema labarai a yau ranar Asabar, kwamishinan ƴansandan jihar Kano, Usaini Mohammed Gumel, ya jaddada ƙudirin rundunar na biyayya ga umarnin kotu da kuma wanzar da zaman lafiya. Ya kuma gargaɗi masu son tayar da fitina da su shiga taitayinsu tare da tabbatar wa jama’a cikakken haɗin kan ƴansanda da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya.
Kwamishinan ya bukaci al’ummar Kano da su kwantar da hankulansu kuma a mutunta doka domin kotu za ta yi magana a ranar 3 ga watan Yuni 2024. Ya kuma ƙara da cewa duk wanda ya yi yunkurin kawo cikas ga zaman lafiya zai fuskanci hukunci mai tsanani a shari’a, saboda ƴan sanda da sauran jami’an tsaro. a shirye suke don tunkarar duk wata barazana da kwanciyar hankali.