Babban basaraken karamar hukumar Mbo a jihar Akwa Ibom, Ogwong Okon Abang, ya samu ‘yanci bayan da wasu masu garkuwa da mutane suka yi garkuwa da shi har na tsawon mako guda. Majiya mai tushe ta tabbatar da cewa an sako shi ne jiya Lahadi, 26 ga watan Mayu, 2024, biyo bayan biyan Naira miliyan 50 na kudin fansa.
Tun da farko dai wasu ‘yan bindiga ne suka yi garkuwa da Sarkin gargajiyar har masarautarsa da ke unguwar Ebughu a bakin kogi. Masu garkuwa da mutanen sun yi taho-mu-gama da shi a cikin wani jirgin ruwa mai gudun gaske, wanda da cikin sauri ya bace bayan sace Sarkin ta gabar tekun Ibaka zuwa cikin babban teku.
- Matsayar Ƙungiyar Sarakunan Arewa A Tsaya Kan Umarnin Kotu Kan Rikicin Sarki 2 A Kano
- ‘Yan Majalisar Tarayya Sun Goyi Bayan Gwamnatin Kano Kan Mayar da Sarki Sanusi II
Kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Timfon John, domin jin ta bakinsa ya ci tura, amma majiya daga iyalan Sarkin sun tabbatar da cewa sai da aka biya Naira miliyan 50 kafin aka sako shi, nan take kuma aka garzaya da shi asibitin kwararru domin samun kulawar gaggawa.