Ƙungiyar likitocin jihar Kano LAGGMDP, ta ce tana shirin tsunduma yajin aikin gargaɗi na makonni biyu, daga ranar 19 watan Yuni, matuƙar gwamnatin jihar Kano ta gaza biya musu buƙatunsu.
Da yake ƙarin bayani sakataren ƙungiyar Dakatar Anas Idris, ya ce matuƙar gwamnatin bata biya albashin likitocin da ta ɗauka su 61 a shekarar da ta gabata albashin su na wata biyu wato Oktoba da November, da suka gabata.
- Saurayi Da Budurwarsa Sun Sace Kayan Lefen ’Yar Uwarsa A Kano
- 13 Ga Wata Za A Yanke Hukuncin Hurumin Shari’ar Sarkin Kano
Gidan Radiyo Dala ya rawaito cewa, Dakta Anas ya ce akwai buƙatar gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf, ta yi duba akan tsaron lafiyar likitocin yayin da suke bakin aiki, domin kula da lafiyar su.