A ranar Juma’a ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana sunan Sadiq Aminu Wali a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Kano.
Jam’iyyar PDP a jihar ta rabu gida biyu, inda ko wane bangare ya gudanar da zaben fidda-gwani na jam’iyyar wanda ya haifar da Saqi Wali da Mohammed Sani Abacha dan marigayi shugaban mulkin soja a matsayin ‘yan takarar gwamna.
- Cikin Watanni Uku An Haifi Yara Sama Da 27,000 A Kano
- Yajin Aikin ASUU: Gwamnati Ta Bukaci Kungiyar Kwadago Ta Fasa Yin Zanga-Zanga
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da bangaren Shehu Sagagi da ya gabatar da Mohammed Abacha a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar a jihar.
Sai dai a wani yanayi na daban, ofishin na INEC na Kano a yau Juma’a, ya fitar da sunan Wali tare da abokin takararsa, Yusuf Dambatta a matsayin ‘yan takarar gwamna da mataimakinsa a zaben 2023.
Abba Kabir Yusuf, wanda ke daga tutar jam’iyyar , NNPP, shi ma ya shiga jerin sunayen tare da abokin takararsa, Aminu Abdulsalam.
Haka shima dan takarar gwamna a jam’iyyar PRP, Salihu Tanko Yakasai, sunansa ya fito.
Sannan Sheikh Ibrahim Khalil, sunansa ya fito a matsayin dan takarar gwamna a jam’iyyar ADC.