A yau Juma’a ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya gana da wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
LEADERSHIP ya tattaro cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar mai mulki, Bola Tinubu, bai halarci taron ba.
- Nasarar Yaki Da Hanci A Kasar Sin
- INEC Ta Maye Sunan Mohammed Abacha Da Sadiq Wali A Matsayin Dan Takarar PDP A Kano
Hakazalika, babu wani daga cikin gwamnonin jahohin yankin kudu maso yamma da kuma shugaban majalisar wakilai halarci zauren majalisar don shiga taron.
A daya bangaren kuma taron ya samu halartar shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan; mataimakin kakakin majalisar wakilai, Idris Wase; shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu; da kuma mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Sanata Kashim Shettima.
Sauran sun hada da shugaban kungiyar gwamnonin APC, gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu; gwamna Babagana Zulum na jihar Borno; gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe; gwamna Muhammad Yahaya na jihar Gombe; gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa, tsohon ministan Noma, Audu Ogbeh da tsohon kakakin majalisar wakilai, Dimeji Bankole.
A nasa jawabin, mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, ya bayyana cewa Tinubu bai halarci taron ba ne sakamakon matsalar jigilar jirage da ake fuskanta sakamakon tsadar man jiragen.
Ya shaida wa shugaba Buhari cewa jam’iyyar na da aniyar kwankwasa kofarsa don neman shawara, tare da yin la’akari da sunan shugaban kasar domin samun nasarar jam’iyyar APC a zaben 2023 mai zuwa.