Hukumar karbar korafe-korafen jama’a da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta fara binciken sama da faɗi a cikin shirin tallafawa masu sana’ar a bakin tituna da aka ƙaddamar kwanan nan.
Shirin wanda ke da nufin baiwa masu sana’a 465 Naira 50,000 kowannensu, amma rahotanni suka bayyana cewa wasu mutane sun yi shigar kura da fatar Akuya a matsayin wadanda suka ci gajiyar tallafin.
- Ƙungiyar Likitocin Kano Za Ta Tsunduma Yajin Aiki
- Gwamnatin Kano Ta Biyawa Ɗalibai 119,903 Kudin Jarrabawar NECO Da NBAIS
Wani faifan bidiyo ya nuna yadda ake gabatar da wasu mutane masu da’awar suna cikin waɗanda aka ware don ba wa tallafin.
Shugaban hukumar Barista Muhuyi Magaji Rimingado ya tabbatar da gudanar da binciken a yau Lahadi, inda ya ce hukumar za ta tabbatar da hukunta waɗanda ke da hannu a lamarin.
Ya bayyana cewa ana gudanar da binciken ne a ƙarƙashin sashe na 21, 22, da 23 na dokar hukumar, wanda ya shafi ayyukan damfara da karkatar da kudade.
Rimingado ya jaddada cewa binciken ba wai akan wasu mutane ne aka yi niyya ba amma wani bangare ne na ƙoƙarin da ake na binciko ayyuka daga gwamnatocin baya da na yanzu.
Muhuyi ya yi kira ga jama’a da su bayar da duk wasu bayanansu da kara karfafa gwiwar ci gaba da bayar da goyon baya ga hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.