An bayyana cewa, sirrin da ke tattare da nasarar da Hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna ke ci gaba da samu a aikin hajjin bana ya samo asali ne daga shiriya daga Allah (SWT) da kuma taimako da goyon bayan Gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Uba Sani ga shugabannin hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin Shugaban Shashin gudanarwar ɓangaren kimiyyar sadarwa na hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna, Abubakar Usman Yusuf, ya ce, bayan goyon baya da hukumar ta samu ta kuma yi sa’ar samun tsayayyen shugaba, wato Sheikh SS Abubakar, waɗannan sune suka taimaka muka yi zarra a tsakanin sauran jahohi.
- Hajjin 2024: Wani Alhaji Dan Nijeriya Daga Jihar Kebbi Ya Rasu A Makkah
- Jirgin Ƙasan Kaduna Zuwa Kano Zai Fara Aiki Farkon 2025
Ya ƙara da cewa, da farko dai mun tabbatar da zaƙulo kwararrun ma’aikata domin su riƙe dukkan madafun aiki a bangarori daban-daban na tafiyar da ayyukan alhazai tun daga gida har zuwa kasa mai tsari, musamman abin da ya shafi masaukansu da abincin da za su ci da zaman da za su yi a Muna, da Muzdalifah da kuma Arafat.
Wannan shi ne ginshikin nasarar, mun kuma yi ƙoƙarin ilimantar da alhazai a kan yadda abubuwan suke da kuma irin goyon bayan da muke bukata daga gare su.
Haka kuma mun jawo masu ruwa da tsaki a harkokin tafiyar da aikin Hajjj a gida Nijeriya da kuma Saudiya, inda muka bukaci samun goyon bayan su domin samu nasara.
“Tuni muka kuma tura jami’anmu yankunan Masha’ir don su kalli yadda za a tafiyar da zama a wurare kamar su Muna, Muzdalifa da Arafat, mun shirya alhazai a tsarin mutum arba’in-arba’in da kuma ƙananan hukumomi domin samun cikakkiyar nasara” in ji shi.
A kan batun katin NUSU, ya ce kusan dukkan alhazan jihar Kaduna sun samu katin su, waɗanda ma basu samu a nan gaba kadan katinsu zai shiga hannun su.