Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta hada hannu da kungiyar kasuwar hada-hadar wayoyin hannu ta jihar domin dakile matsalar sace-sace da kwace waya da ya addabi kwayar birnin jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan Kano, Sama’ila Dikko, ne ya tabbatar da hakan a lokacin da kungiyar ta kai masa ziyara da kuma ba shi lambar girma a ofishinsa.
- Farashin Alkama Ya Sauka a Duniya
- Kotu Ta Dage Shari’ar Wanda Ake Zargi Da Auran Jikarsa A ZamfaraÂ
Kwamishinan ya ce ya yi matukar farin ciki bisa yadda kungiyar ta yi kudirin hada hannu da rundunar domin ganin an dakile ta’adar sace-sacen wayoyi, musamman a wannan lokaci da lamarin ya addabi al’ummar jihar Kano.
Samaila Dikko, ya ce kofarsu a bude take wajen yin mu’amala da kungiyar duba da yawan kasuwannin siyar da wayoyin da ke Kano, inda ya ce kungiyar za ta taka rawar gani wajen zakulo bata-garin ta hanyoyi daban-daban.
Tun da fari, a jawabinsa shugaban gamayyar kungiyoyin hada-hadar wayoyin hannu ta jihar Kano, Alhaji Ahmad Tijjani Usman, ya ce Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, ya gayyaci kungiyar domin tattauna wa da ita kan zargin da ake yi wa ‘yan kasuwar wayoyin hannu.
ya ce ana zargin ana hada kai da masu sayar da wayoyin domin sayar da wayoyin da aka sato ko kwato, inda ya ce ya ce wannan zargi ba haka ya ke ba domin suma suna iya bakin kokarisu don ganin basu sayi wayar da aka sato ko aka kwato ba.
Shugaban kungiyar ya bayyana cewa za su ba da gudunmawarsu don kawar da wannan dabi’a da matasa ke yi a fadin jihar.
Shugaban ya ce kungiyar ta samar da cikakken kwamiti na musamman domin bibiyar masu shigo wa kasuwannin wayoyin hannu domin sayar da wayoyin da suka kwata ko sata domin Idan ba a sayen wayoyin dole barayin su daina satowa.
Ya kuma ba da lambobin karta-kwana ga duk wanda a ka sace wa ko kwace wa waya domin gano wadanda su ka aikata cikin gaggawa.
Lambobin sune ;08065416459 ko 08039725508 ko kuma [email protected].