Kasurgumin dan bindigar da ya addabi jihohin Zamfara da Katsina, Ado Aleiro, wanda a baya-bayan nan aka yi wa sarautar Sarkin Fulanin ‘Yandoton, ya yi ikirarin cewa ba ya garkuwa da mutane face kawai kisa yake yi.
Nadin sarautar Aleiro wanda shi ne jagoran ‘yan ta’adda a Tsafe da Faskari a jahohin Zamfara da Katsina, ya jawo cece-kuce a fadin kasar nan.
- Wayar Da Kai: INEC Za Ta Hada Hannu Da Kungiyar ‘Darika Awareness Forum Katsina’
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Kansila A Adamawa
Daga bisani gwamnatin jihar ta dakatar da Sarkin garin, Aliyu Marafa, wanda ya bai wa Aleiro sarautar, wanda ake nema ruwa a jallo a makwabciyar jihar Katsina bisa laifin kashe-kashen jama’a.
Gwamnatin Katsina ta bayar da tukuicin Naira miliyan biyar kan bayanan da suka kai ga kama Aleiro, wanda ake zargi da kashe mutane 52 a garin Kadisau da ke karamar hukumar Faskari a shekarar 2019.
Aleiro ya shaida wa BBC cewa ya fusata da Hausawa da gwamnatin Nijeriya.
Aleiro ya ce yayin da mutanensa ke garkuwa da mutane, shi kuma ya fi sha’awar kashe mutane ne kawai.
“Mutane ke garkuwa da mutane; ni ina zuwa na kashe su ne (mutane),” in ji Aleiro.
Wani na hannun daman Aleiro da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa tawagar ‘BBC Africa Eye’ cewa “An cire Fulani daga ayyukan gwamnati da sauran abubuwan da suma shafi tattalin arziki, kuma sojojin saman Nijeriya na kai hari ga Fulani makiyaya da kuma kashe musu shanu.
“Ta yaya Fulani suka zama marasa kima haka a Nijeriya?” Kamar yadda ya tambaya.
Ya koka da yadda aka rufe hanyoyin kiwo, wanda da su Fulani suka dogara yayin da kasa da ruwa suka yi karanci.
Mun Sayi Makamai Da Yawa – Wadanda Suka Sace Daliban Makarantar Jangebe
BBC ta kuma yi hira da ‘yan ta’addan da suka sace daliban makarantar sakandaren mata ta gwamnati da ke Jangebe a karamar hukumar Talata Mafara a jihar Zamfara.
Yayin da gwamnatin jihar ta ce ba ta biya kudin fansar daliban mata ba, wani dan bindiga da ba a bayyana sunansa ba, ya ce an biyansu Naira miliyan 60 kafin su sako daliban.
Da aka tambaye shi me suka yi da kudin, sai ya ce, “Mun kara sayen bindigogi.”
An kuma fitar da al’amuran da suka tada hankali ciki har da na wani yaro da ya mutu sakamakon harbin bindiga a lokacin da suka sace daliban.
“Na tuna yadda ya daga kai ya dube ni yayin da yake cikin wannan hali,” mahaifin yaron ya shaida wa BBC.
“Abun ya min zafi yadda yarona ya sha wahala…Na yi bakin ciki.”
BBC ta tattaro cewa matashin wanda ‘yar uwarsa na cikin ‘yan matan makarantar Jangebe da aka sace, jami’an tsaro ne suka kashe shi.
Wani bangare na binciken da tawagar ‘Documentary’ ta gudanar, shi ne yadda al’ummar Hausawa ke ci gaba da zaluntar al’ummar Fulani, wanda ya bayyana a haduwar tawagar da mazauna yankin Kurfar Danya.
“Idan aka yarda, za mu kashe kowane Bafulatani, ko da a cikin gari ne,” in ji wani daga cikin ‘yan banga, “saboda sun kashe iyayenmu, yaranmu, sun jefar da gawarwakinsu a nan.”
Wani mazaunin garin ya bayyana rashin amincewa da kisan da ‘yan ta’adda suka yi wa mutane sama da 200.
Mazauna yankin sun kai dan jaridar BBC zuwa wuraren da birne mutane.
Haka zalika an kara tabbatar da cewa tashe-tashen hankula a yankin na da nasaba da daukar fansa, maimakon kariya.
Kungiyoyin ’yan banga galibi mazauna al’ummar Hausawa ne.
“A bayyane yake cewa kabilanci ne,” in ji Hassan, wani dan ta’adda wanda yana daya daga cikin Fulanin farko da suka fara shigo da bindigogi cikin Zamfara tare da daukar makamai karkashin wata kungiyar ta’addanci.
“Idan ba haka ba, me zai sa Bafulatani ya kashe Bahaushe wanda bai masa komai? A bayyane abun yake, rikici ne na kabilanci.”
An sha yin maganganu cewar hare-haren ‘yan bindiga a wasu jihohin arewa maso yamma na da alaka da rikicin kabilanci ko kuma daukar fansa, wanda hakan ta fi faruwa a tsakanin ‘yan bindigar da ‘yan banga ko kuma ‘yan sa-kai a jihohin Zamfara da Katsina.