Wani Alhaji mai suna Malam Abba Limawa mai shekara 52 ya tsinci makudan kuɗaɗen ƙasashen waje amma maimakon ya rike domin amfanin kansa sai ya mika wa hukumar kasar Saudiya. Kudaden sun hada da Dalar Amurka 800 da Riyal 650 da kuma kudin kasar Rasha 10,500.
Alhajin mai shekara 52 ya fito ne daga ƙaramar hukumar Dutse, shugaban hukumar Alhazai na Jihar Jigawa ne ya gabatar da shi a taron kammala aikin Hajjin bana da hukumar Alhazai ta kasa NAHCON ta shirya ranar Laraba a Makka,
- An kammala Aikin Hajjin Bana 1445/2024
- Hajjin Bana: Zafi Ya Yi Ajalin Alhazai Sama Da 900 A Saudiyya
Bayanai sun nuna cewa, Alhajin ya tsinci kuɗaɗen ne a yayin da ya shiga banɗaki a masallacin Harami, “Da farko na so in yi watsi da jakar, in yi tafiyata amma sai na ce a zuciyata, jakar na iya zama ta wani tsoho ko tsohuwa ‘yan Nijeriya, kuma yana can cikin tashin hankali, daga nan ne na ɗauki jakar na miƙa wa jami’an hukumar Alhazai ta jihar mu.
A jawabinsa, shugaban hukumar Alhazai ta Nijeriya NAHCON, Malam Jalal Ahmed Arabi ya yaba wa halayyar Alhajin ya kuma nemi Alhazai su yi koyi da Alhaji Abba Limawa.