Shugaban hukumar hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta ƙasa (NDLEA), Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa mai ritaya ya bayyana dabarun da hukumar ta ke bi na kai hari kan kadarorin manyan masu dillalan kayan maye da masu safarar miyagun kwayoyi a wani taron manema labarai a Abuja.
Taron yana a matsayin wata alamar fara ayyukan da za a shafe mako guda don ranar yaƙin sha da fatauci kayan maye a Duniya na 2024. Marwa ya jaddada cewa kwace kadarorin wani muhimmin ɓangare ne na yaƙi da ayyukan miyagun kwayoyi da ruguza dabarsu.
- Mun Cafke ‘Yan Kwaya 50,901 Da Gurfanar Da 9,034 A Shekara 3 – Marwa
- Ba Za A Tabbatar Da Kwanciyar Hankali A Yankin Gaza Ba Har Sai Amurka Ta Daina Samarwa Isra’ila Da Makamai
Marwa ya bayyana nasarar shirin hukumar NDLEA mai suna War Against Drug Abuse (WADA), wanda ke amfani da cikakkiyar tsarin rigakafin gurbacewar al’umma.
Ya jaddada cewa wannan shiri ne na bayar da shawarwari, da wayar da kan jama’a tare da karfafa haɗin gwuiwa a kan sha da fataucin muggan kwayoyi. Wannan ya yi dai-dai da taken ranar sha da fataucin miyagun kwayoyi ta duniya ta shekarar 2024: “Shaida a bayyane take: Zuba Jari a Rigakafin,” wanda ke nuna muhimmancin matakan kariya don hana mutane yin ta’ammali da magunguna.
Da yake nuna godiya ga gwamnatin tarayya da ta jihohi da masu ruwa da tsaki daban-daban bisa goyon bayan da suka bayar, Marwa ya yi karin bayani kan ƙoƙarin haɗin gwuiwa da abokan hulɗar ƙasa da ƙasa da suka hada da ofishin MDD kan yaƙi da miyagun kwayoyi (UNODC), hukumar yaƙi da fataucin miyagun kwayoyi ta Amurka (DEA), da sauransu.
Mataimakin wakilin UNODC, Mista Danilo Campisi, ya buƙaci a ƙara bin duk matakan rigakafin domin daƙile hasashen ƙaruwar amfani da miyagun kwayoyi da kashi 40 cikin 100 nan da shekarar 2030, musamman a tsakanin matasa.
Taron ya jaddada muhimmancin ci gaba da inganta dabarun rigakafi shigowa da fara amfani muggan kwayoyi a cikin al’umma.