Gwamnatin Tarayya ta karyata ikirarin da ake yi na cewa ana tsare da jami’in Binance, Tigran Gambaryan cikin yanayi mara kyau inda yake fuskantar matsala game da lafiyarsa.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa Mohammed Idris, ya jaddada cewa wadannan zarge-zarge ba su da tushe balle makama, inda ya bayyana cewa Gambaryan yana samun ingantacciyar kulawa game da lafiyarsa.
- Ya Kamata A Karfafa Manufar Amfani Da Harsunan Gado A Makarantu
- Falalar Ziyarar Kabarin Annabi S.A.W (1)
Idris ya ba da tabbacin cewa kotu ce ta bayar da umarnin tsare jami’in na Binance kuma kotu ce kawai ke da hurumin sauya sharudan tsare shi ko kuma sakin sa.
Ya nanata kudurin Nijeriya na kiyaye muhimman hakkokin Gambaryan, da suka hada da samun ingantaccen kiwon lafiya, yayin da yake fuskantar shari’a kamar yadda dokar Nujeriya ta tanada.
Ministan ya bayyana yadda Nijeriya ke bin ka’idojin shari’a da diflomasiyya a shari’ar da ta ke yi a kan kamfanin Kirifto na Binance.
Ya kuma jaddada kudirin gwamnati na tabbatar da adalci da kuma kiyaye mutuncin shari’a, tare da tabbatar da kare hakkin Gambaryan na shari’a da na dan Adam a tsawon lokacin shari’ar.