An sake samun wani mahajjaci dan Nijeriya daga jihar Zamfara ya tsinci makudan kudade da yawan su ya kai 1,750 na kudin Yuro, wadanda suka haura Naira Miliyan biyu da dubu dari takwas a kudin Nijeriya.
Mutumin mai suna Malam Muhammadu Na’Allah daga Karamar Hukumar Gumi ta jihar Zamfara ne ya tsinci kudaden a masallacin Harami da ke Makkah a lokacin da ya je Sallah.
- Alhajin Jihar Jigawa Ya Mayar Da Makudan Kudaden Da Ya Tsinta Ga Mai Shi A Makka
- Hajjin 2024: Wani Alhaji Dan Nijeriya Daga Jihar Kebbi Ya Rasu A Makkah
Malam Na’Allah bayan ya yi tozali da makudan kudaden sai ya yi gaggawar sanar da shugaban hukumar alhazai ta jihar Zamfara, inda suka garzaya gaba dayansu zuwa ofishin Hukumar NAHCON da ke birnin Makkah suka kai kudaden domin a mika su zuwa hukumar aikin Hajji ta kasar Saudiya.
Malam Jalal Ahmad Arabi ya yaba wa, Malam Muhammadu Na’Allah, a kan wannan babban abun kirkin da ya aikata tare da jinjina masa kan wannan aikin da zai kara fito da darajar ‘yan Nijeriya a idanun duniya.
Kamar yadda daya daga cikin jami’an yada labarai ‘yan Nijeriya daga kasa mai tsarki, Malam Rabi’u Biyora, ya wallafa a shafinsa na facebook ya ce tuni har an tuntubi Hukumar Aikin Hajji ta Saudiya da makudan kudaden.